GWAMNATI DA LIKITOCI SUN CI WA JUNA KWALA: Sun bar marasa lafiya ‘mutu kwakwai rai kwakwai’

0

Kalamai marasa dadin ji da Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Likitoci ta NARD ke antaya wa juna, yanzu dai talakawa da marasa galihu da ba su iya zuwa asibitin kuɗi lamarin ke addaba.

Yayin da likitocin su ka ce ba za su koma aiki ba, har sai Gwamnantin Tarayya ta biya su haƙƙoƙin su domin su samu damar ɗaukar ɗawainiyar riƙe iyalan su, ita kuma Gwamnantin Tarayya ta ce duk likitan da bai koma bakin aiki ba, to ya fitar da rai daga karɓar albashin sa.

Na Ce Kada A Biya Likitoci Albashi Sai Sun Koma Bakin Aiki -Minista Ngige:

A wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Ministan Ƙwadago Chris Ngige ya furta cewa ya bada umarnin kada a biya duk wani likita da ke aiki a ƙarƙashin gwamnanti albashin sa, in dai ya tafi yajin aiki, har sai ranar da ya koma za a fara lissafi.

“Likitocin nan fa sun raina Najeriya. Na kuma bada umarnin idan su ka ƙara kwana bakwai ba su koma ba, to duk za a kore su.”

Wannan wa’adin dai zai ƙare ne a ranar Litinin mai zuwa ta gobe.

Minista Ngige Karan-kaɗa-miya, Mun Fi Ƙarfin Tsayawa Faɗa Da Shi -Likitocin NARD:

Shugaban Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa (NARD), Okhuaihesuyi Uyilawa, ya bayyana wa Minista Ngige cewa shi fa ba kowa ba ne sai ministan ƙwadago.

Ya ce Ngige ya daina cika baki da hura hanci, tunda ba shi ne Shugaba Muhammadu Buhari ba.

Batun janye yajin aiki kuwa, Uyilawa ya ce ba za su koma ba. “Sai dai a fara biyan mu haƙƙin mu tukunna kafin mu koma. Tunda dai mun lura wannan gwamnati ba mai cika alkawarin yarjejeniyar da mu ke ƙullawa ba ce.

“Sannan mu fa mun fi ƙarfin a yi mana barazana da kora. Idan ya sa an kore mu sai me, tunda ba biyan mu haƙƙin mu ake yi ba? Kuma ba shi ne farkon fara korar likitoci ba. Tsakanin 2010 da 2014 Ministan Lafiya na lokacin Onyebuchi Chukwu ya kori likitoci daga aiki. Saboda haka idan yanzu Ngige ya kore mu, ba kan sa farau ba. Wancan lokacin da aka kori likitoci ai asibitocin ƙasar nan kusan durƙushewa su ka yi.

“Yanzu ma idan Ngige ya kore mu, ya zama Ministan da ya kori likitoci don sun nemi a biya su haƙƙin su.”

A makon jiya dai PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Buhari da likitocin Najeriya su ka ƙaurace wa asibitocin ƙasar nan lokaci guda.

Kamar jira su ke yi Shugaba Buhari ya tafi Landan ganin likita, su kuma Ƙungiyar Likitoci ta NARD sai su ka tsunduma yajin aikin da su ƙaurace wa asibitocin ƙasar nan, ko allura su ka daina yi wa majiyyata.

A makon da ya gabata dai Shugaba Buhari ya yi kwanaki fiye da 200, jimlace a Landan da sunan zuwa ganin likita, a tsawon shekaru shida da ya shafe a kan mulki.

Asibitocin ƙasar nan da dama sun wayi garin Litinin da yajin aikin likitocin da ke ƙarƙashin ƙungiyar NARD. Wakilan PREMIUM TIMES sun zagaya asibitoci a garuruwa daban-daban, kuma sun tabbatar da haka.

A Asibitin Gwamnantin Tarayya na Legas da ke Ebute-Metta, wakilin mu ya samu likita ɗaya tal ya ganin marasa lafiya sama da 300, a ranar Litinin ɗin da aka fara yajin aikin.

Wani da ya zanta da shi, ya ce ya kai matar sa asibitin ne, kuma ita ce ta 45 a layi. “Amma kuma har zuwa yanzu ƙarfe 3 na yamma ba a zo kan ta ba. Wasu ma duk sun koma gida a fusace, kuma cikin damuwa.” Inji Inanaco.

A Abuja kuwa, wakilin mu ya leƙa Babban Asibitin Ƙasa, wanda Najeriya ke ji da shi, kuma na fita-kunya.

Wani mai suna Lucky Oche da ke jiyyar mahaifin sa, ya shaida wa wakilin mu cewa marasa lafiya a asibitin hankulan su a tashe ya ke. “Saboda kowa tsoro ya ke ji idan yajin aikin ya daɗe, za a sallami da wanda ya ji sauƙi da wanda bai ji ba, duk a sallame su baki ɗaya.”

Kusan haka lamarin ya ke s yawancin asibitocin ƙasar nan tun daga ranar Litinin, kuma alamomi na nuna cewa lamarin ya na ci gaba da dagulewa.

Likitocin dai sun tafi yajin aiki ne saboda gwamnatin tarayya ta ƙi cika masu alƙawarin da ta ɗauka t CTun cikin watan Afrilu, bayan sun shafe watanni a baya su na gargajiya kafin a kai ga ɗaukar alƙawarin.

Share.

game da Author