GWAMNAN APC YA KALUBALANCI BUHARI: Ka saka dokar ta baci a jihohi, idan kana son a gama da ‘yan bindiga

0

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ya kalubalanci shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya saka dokar ta baci a wasu jihohin Arewa idan har ana so a kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga a yankin.

Kakakin gwamnan jihar ya fidda wannan sanarwa a wata takarda ranar Alhamis bayan ganawar gwamna Matawalle da Mataimakin Sufeto Janar din ‘yan sanda dake kula da yankin Zamfara, Sokoto da Kebbi, Ali Janga bayan ya ziyarce shi a jihar.

Matawalle ya ce matsalar tsaro ya yi matukar tsanani a jihar da yankin wanda abinda ya fi da cewa shine shugaba Muhammadu ya saka dokar ta baci a harkar tsaro a wasu jihohin kasar nan idan har ana son a ga bayan tsananin rashin tsaro da ake fama da shi.

” Yanzu kowa a yankin nan a tsorace yake, yana cikin fargaba, dole sai an dauki wani mataki mai tsaurin gaske wanda ba a saba da shi ba idan ana so a ga bayan wannan matsala.

” Matsalar jihar Zamfara ya wuce abinda ake tunani, abin yayi tsanani sosai, dole a karkato zuwa jihar da sauran jihohin yankin domin abin yana neman ya fi karfin kowa yanzu saboda kulle-kullen da ke cikin sa.

Jihohin Arewa Maso Yammacin Najeriya, da suka hada da Kaduna, Zamfara, Sokoto da Kebbi na fama da tsananin rashin tsaro a yankin.

Share.

game da Author