Gwamna Lalong ya roƙi Fulanin Ondo da Gwamnatin jihar su yafe kisan da ɓatagari su ka yi wa matafiya a Jos

0

Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya roƙi Fulanin Jihar Ondo da kuma Gwamnatin Ondo su yafe kisan da wasu ɓatagari su ka yi wa matafiya 23 a Rukuba, Jos.

Kisan dai ya faru a ranar 14 Ga Agusta, inda matasan Kiristoci su ka kashe Fulani Musulmai waɗanda ke kan hanyar komawa garin su a Jihar Ondo, bayan sun halarci taron murnar zagayowar shekarar Musulunci a gidan Sheikh Ɗahiru Bauchi, a garin Bauchi.

Rahotanni sun tabbatar da an kashe mutum 23, an i wa 23 raunuka, kuma jami’an tsaro sun kuɓutar da fiye da mutum 30.

Gwamna Lalong ya tura ƙaƙƙarfar tawaga zuwa Ondo, a ƙarƙashin Mataimakin Gwamnan Filato, Sonny Tyaden zuwa Jihar Ondo domin yin ta’aziyya ga Gwamnatin Ondo da kuma iyalan waɗanda aka kashe wa ‘yan’uwa da iyaye.

Sun kuma tafi da sauran waɗanda aka kuɓutar ɗin su ka kai su har Jihar Ondo.

A cikin tawagar akwai Mai Martaba Sarkin Wase, Muhammad Haruna, Shugaban Miyetti Allah na Jihar Filato, Nura Mohsmmed da kuma Shugaban Yarabawa mazauna Jihar Filato.

Lalong ya shaida wa Gwamnatin Ondo da Fulanin cewa ba da yawun Gwamnantin Filato ko al’ummar jihar aka kashe Fulanin ba.

Ya ƙara da cewa wasu ɓatagari ne, kuma jami’an tsaro sun Kama wadanda ake zargi, za a hukunta su.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na bakin ƙoƙarin ganin irin wannan mummunan lamari bai ƙara faruwa ba.

Gwamna Rotimi Akeredolu ya gode wa Lalong dangane da matakan da ya ɗauka, wajen ganin kisan bai fantsama har an ƙara yin asarar wasu rayuka ba.

Akeredolu ya ce lokacin da lamarin ya faru, ya gaggauta hanzartawa kasuwar sayar da shanu, inda ya samu shugabannin Fulanin, ya yi masu ta’aziyya, jimami da alhini.

Akeredolu dai Mataimakin sa Lucky Aiyedaruwa ne ys wakilci shi wajen karɓar tawagar.

Mun Yafe Ba Za Mu Ɗauki Fansa Ba -Fulanin Ondo

A jawabin sa, Shugaban Ƙungiyar Fulani Mazauna Kudu Maso Yamma, Kabiru Mohammed ya shaida wa tawagar cewa sun yafe, kuma ba za su ɗauki fansa ba.

A jawabin sa, ya ce zaman lafiyar wannan ƙasa na gaba da komai, don haka ba za su ƙullaci wasu da niyyar yin ramuwar-gayya ba.

Shi da Gwamnatin Ondo sun gode ganin yadda tawagar gwamnatin Filato ta maida sauran matafiyan gidan su a jihar Ondo.

Share.

game da Author