Kamar yadda ya saba taimakon bayin Allah, da gabatar da ayukkan jinkai a wurare daban-daban, a yau Laraba ma, wato 04/08/2021, Maulanmu Khalifan Tijjaniyyah a Najeriya, Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II, karkashin wakilci, da jagorancin Mai girma Falaki, Alhaji Mujtaba Abba, ya biya wa wasu bayin Allah da suke zaune a gidajen yarin Kurmawa da Goron Dutse, tsabar kudi har naira miliyan ashirin da daya, da dubu dari bakwai da casa’in da bakwai, da dari shida (N21,797, 600), domin su shaki kamshin ‘yanci kamar kowane Dan Adam mai cikakken ‘yanci. Muna addu’a da rokon Allah ya sakawa Mai Martaba Sarki da mafificin alkhairi, duniya da lahira; kuma yadda yake kokari, kuma yake fadi-tashi, ba-dare-ba-rana, wurin taimakon bayin Allah, shima muna yi masa rokon Allah yaci gaba da taimaka masa a cikin dukkanin lamurransa da yasa gaba, amin.
Yadda lamarin ya wakana, shine kamar haka: a gidan yarin Kurmawa, akwai Mutum goma sha hudu (14) da aka biya wa bashin kudi da ake bin su, domin su samu fita daga wannan kangi, na wannan gida da Allah ya jarabe su da shiga cikinsa. Kudin da aka biya masu jumlatan sune: Naira miliyan goma sha hudu da dari bakwai da saba’in da tara (N14, 779, 000:00).
Daga kurkukun Kurmawa tawagar Mai girma Falakin ta zarce zuwa gidan yarin Goron Dutse, inda aka biya wa mutum ashirin da hudu (24) maza, da ashirin (20) Mata bashin da ake bin su. Su ma cikin taimakon Allah, an biya masu bashin kudaden da ake bin su, domin su koma gidajensu, cikin mutunci da ‘yanci da walwala. An biya Naira miliyan bakwai da dubu goma sha takwas da dari shida (N7, 018, 600:00).
Muna kara addu’a da rokon Allah ya taimaki Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifah Malam Muhammadu Sanusi II, Allah ya kara masa lafiya da imani da tsawon rai mai albarka, kuma mai amfani, amin.
Kuma wadanda aka biya wa bashin sun hada da maza da mata, musulmai da kiristoci.
Sannan Mai Girma Falaki Alhaji Mujtaba Abba, yayi kira, da yin nasihohi masu muhimmanci matuka, ga wadannan bayin Allah da suka amfana da wannan tausayi da jinkai na Mai Martaba Sarki, akan su yi kokari su zama kyawawan ambasadoji, kuma wakilai nagari a cikin al’ummominsu, sannan ya shaida masu cewa, kada su zata cewa ko don Allah baya son su ne, shi yasa aka kai su gidan yarin; ya nuna masu ba haka lamarin yake ba. Yace shi shiga gidan yari al’amari ne na kaddara daga Allah, kuma ya kara da cewa, gidan yari wuri ne da in mutum ba da hakkinsa ya shiga ba, to tabbas kamar wata daukaka ce, da wani babban al’amari na rayuwa zai hadu da shi a gaba, kamar yadda duk mun san kissar Annabin Allah, Annabi Yusuf Alaihis-salamu yadda ta kasance.
Sannan mai girma Falakin yaci gaba da cewa, gidan yari wuri ne da zai sa mutum ya waiwaya baya, domin yayi kokarin samun nasara a rayuwarsa ta gaba, kuma domin mutum yayi kokarin gyara wuraren da yake da kura-kurai a cikin rayuwarsa. Sannan yace wata dama ce ta kara kusanci ga Allah (SWT), tun da ana wuri guda da zai taimakawa mutum yayi ibadu; kamar karatun Alkur’ani mai girma da sauran littafai na ilimi, da kokarin yawaita nafilfili, da koyon sana’oi.
Sannan Mai girma Falakin, a muhimman jawaban nasa, ya kara da yin wani muhimmin albishir cewa, kamar yadda Mai Martaba Sarki ya saba yi, duk watan Ramadan, ashirin da takwas ga wata (28), Mai Martaba Sarki yake aiwatar da irin wannan gagarumin aiki, don haka In Shaa Allahu, za’a ci gaba da aiwatar da shi kowace shekara. Kamar yadda duk wani abu da Mai Martaba Sarki yake yi na tallafawa bayin Allah, da mabukata, da gajiyayyu, babu wanda ya tsaya ko aka dakatar. Cikin taimakon Allah da huwacewarsa, anci gaba da yi kamar yadda aka saba.
Wannan kamar yadda Allah yake shaida, kuma kowa ya sani, kuma muma mun shaida, duniya ma ta shaida, dama aikin Khalifah ne; duk watan azumin Ramalana, Khalifah yakan kai ziyara da kan sa, gidan gyaran hali, wato gidan yari, domin ya fitar da wadanda karamin laifi ne, ko kuma bashi ya kai su gidan. Kuma duk wadannan ayukka, Mai Martaba Sarki yana yin sune ba don komai ba, sai don saboda Allah, da kuma neman yardarsa.
Kuma babban makasudin gudanar da wannan aiki na alkhairi na yau da aka aiwatar, wato na kubutar da wadannan bayin Allah, ya kasance ne domin kara nuna godiya ga Allah (SWT), da ya raya Mai Martaba Sarki har shekaru 60 masu tarin albarka. Bayan an kammala saukar karatun Alkur’ani mai girma a garin Legas, tare da nuna godiya ga Allah, sai Sarki yace to sai azo a fitar da bayin Allah da suke tsare a gidajen yari, domin kara nuna godiya ga Allah Subhanahu wa Ta’ala akan wannan baiwa da ni’imah.
Allahu Akbar! Kai jama’ah, wallahi ya zama wajibi mu kara jaddada addu’a da rokon Allah ya taimaki Sarki, ya ja zamaninsa; kuma tare da rokon Allah ya karawa Mai babban daki lafiya, da imani, da tsawon rai mai dimbin albarka, amin.
Sannan ina mai addu’a da rokon Allah cewa, Mai girma Falaki, da yake ta kokarin kai komo, shima yake ta fadi-tashi, akan duk wata sabga ta Mai Martaba Sarki, da duk sauran masu taimakawa Sarki wurin aiwatar da ayukkan alkhairin da ya saba aiwatarwa; ayukkan da Allah yake so, kuma ya yarda dasu, irin su Mai girma Danburam, da sauransu, ina rokon Allah ya saka masu da mafificin alkhairi duniya da lahira, amin.
Wassalamu Alaikum
Naku mai kaunar ku, a madadin dukkanin masoyan Mai Martaba Sarki, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Domin karin bayani, za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.