Yayin da Fitaccen ɗan wasa Leonel Messi ya daina buga wa Barcelona ƙwallo, ya koma ƙungiyar PSG ta birnin Paris a Faransa, a yanzu ya zama abokin wasa, aboki kuma abokin burmin mashahuran tsohon mai tsaron bayan Real Madrid, Sergio Ramos.
Ramos ya yi wa Madrid tafiyar bazata zuwa PSG, kamar yadda Messi ya bar miliyoyin magoya bayan Barcelona cikin baƙin ciki da takaici, zuwa PSG.
Waɗannan fitattun ‘yan wasa biyu sun shafe shekara da shekaru a Spain su na buga kwatagwangwamar gurujubjin wasan ƙwararru, wato El-Clasico. Duk wani mai kallon ƙwallo ya san cewa a wasan El-Clasico idan babu Messi, to ba zai yi armashi ba. Haka nan idan Ramos a bayan Madrid, to lamarin bai cika cikakken El-Clasikanci ba.
Babban burin Messi shi ne ya wuce Ramos ko ta halin ƙaƙa ya jefa ƙwallo a ranar Madrid. Shi ma Ramos babban burin sa ya hana Messi cin ƙwallo, ko ta halin ƙaƙa, idan ma ta kama, ya sha sa ƙafa ya shimfiɗar da shi ƙasa kwance shame-shame.
Messi ya zura ƙwallaye a ragar Madrid masu yawa. To sai dai kuma Ramos ya nuna masa cewa shi babbar katanga ce a bayan ‘yan ƙwallo, irin wadda babu kamar ta a yanzu. Domin an shafe kakar wasa ta shekaru huɗu kenan rabon da Messi ya jefa ƙwallo a ragar Madrid.
A yau kuma waɗannan ‘yan wasa gaba ta ƙare a tsakanin su. Mai takalmin ƙarfe ya zama abokin mai katangar ƙarfe. Ƙaƙa-tsara-ƙaƙa!
Idan aka yi la’akari da ‘yan wasan PSG a yanzu, idan aka kira su runduna ko bataliya maimakon ƙungiya, to an yi daidai. Hatsabiban ‘yan wasan su huɗu daga Madrid da Barcelona su ke. Neymar da Messi waɗanda dama tun a Barcelona su biyun su ka firini duniya. Ga kuma Su Maria raina kama ka ga gayya shi da Ramos. Jin sunayen waɗannan ‘yan wasa kaɗai idan aka haɗa da Kylian Mbape zai sa kowane kulob na duniya ya ji shayi ko tsoron karo da su.
Ita PSG dama ta sama sayen ‘yan wasan da su ka shahara a duniya, a daidai lokacin da su ka kusa ritaya daga ƙwallo. Bahaushe dama ya ce kura ko ta zama gurguwa, ta fi ƙarfin kare ya yi wasan langa da ita.
David Beckham ya yi SPG, haka Dani Alves, ɗan wasan da ya fi kowane ɗan wasan ƙwallo a duniya cin kofuna.
To, a yanzu abin da zai fi ɗaukar hankalin masu kallo da masu sharhin ƙwallo a duniya, shi ne ranar da Ramos da Messi za su haɗu da Barcelona da kuma Real Madrid Madrid. A ranakun ne fa za a yi ‘Super El-Clasico’. Ranar da Messi zai ƙure adakar zura ƙwallaye a ragar Barcelona. Sai kuma ranar da Ramos zai dubi ɗan wasan Real Madrid ya shimfiɗe shi a cikin fili kwance tame-tame a ƙasa. Kai, waɗannan ranakun ƙwallo za ta yi daɗin kallo.
Lallai gaskiya ce da ake cewa, ‘gwangwa-da-gwagwa, wai gaɗar giwaye. A ranar ɗan raƙumi sai dai ya tsaya kallo daga gefe.
Discussion about this post