Mafarauta da maharban da su ka fantsama daji domin ceto ɗaliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Yauri a Jihar Kebbi, sun ce sun daina neman yaran haka nan, domin gwamnatin jihar ba ta nuna masu cewa lallai da gaske ta ke yi, ta na so a sako yaran ba.
An dai kama ɗaliban su 102 tun a ranar 17 Ga Maris.
Sun shafe kwanaki 46 kenan a hannun ‘yan bindiga, duk da dai uku sun gudu, wasu uku kuma sun mutu wurin wani ƙoƙarin kuɓutar da su da jami’an tsaro su ka yi.
Idan an tuna, Gwamna Abubakar Bagudu har tara mafarauta ya yi, ya ce ya amince zai shiga gaba ya ja zugar mafarauta domin a ceto ɗaliban.
To sai dai kuma kwanaki 45 bayan yin garkuwa da yaran, Shugaban mafarautan mai suna Ardu Bagobiri, ya sun daina neman yaran, saboda a cewar sa, Gwamnatin Jihar Kebbi ta ƙi tallafa masu da kayayyakin da za su yi amfani su shiga dajin da su, duk kuwa da cewa Gwamna Bagudu ya yi masu alƙawarin haka.
“Mun nemi a ba mu makamai da babura, domin mu riƙa kutsawa cikin surƙuƙin daji. Amma shiru ka ke ji har yau.
“Da farko an ba kowanen mu naira 30,000 aka ce ya bar wa iyalinsa kawai, shi kuma daga baya za a ba shi wani abu. Tun da aka ba mu Naira 5,000 har yau ba a sake ba mu ko sisi ba.”
“Ba fa haka mu ka yi gangami mu ka shiga daji ba. Gwamna ya tara mu, ya sa mana albarka, sannan ya ce zai taimaka mana. Amma shiru ka ke ji.
Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labarai Rabiu Kamba ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Gwamna Bagudu bai manta da su ba. “Takardar neman ba su kayayyakin shiga daji na a kan teburin gwamnan, jira kawai ake yi ya sa hannu.”
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Gwamna Bagudu ya riƙa kurin zai shiga daji ya ceto ɗaliban, amma har yau shiri.
Kurin Gwamna Bagudu Bayan Sace Ɗaliban Yauri 102: Zan Shiga Daji Mu Ƙwato Ɗaliban Kwalejin Yauri
“Hassan Maidaji ƙanen uwa ta ne, zan ja gungun mafarauta mu shiga daji yaƙin ƙwato ɗalibai hannun ‘yan bindiga”
A cikin fushi Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu ya buga gangar gayyatar dukkan mafarautan Jihar Kano domin ya shiga gaba su nausa cikin daji su ƙwato ɗaliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Yauri da ‘yan bindiga su ka yi garkuwa da su.
“Ba mu yi rantsuwa da Alƙur’ani don mu zauna ofis kaɗai ba. Ban rantse da Alƙur’ani a matsayin gwamna don na zauna ofis kaɗai ba. Matsimaki na da sauran Kwamishinoni ba su rantse da Alƙur’ani don su zauna ofis ba.
“Wannan abin da aka yi masa tsokana ce ga Shugaba Muhammadu Buhari. Kuma tsokana ce ga ni Gwamnan Jihar Kebbi.
“Saboda haka na shirya zan sanar da jami’an tsaro cewa zan jagorance ku mu shiga daji domin su Kakkaɓe ‘yan bindiga, kuma mu ƙwato ɗaliban da su ka riƙe.
“Wanda bai sani ba ya sani, Hassan Maidaji ƙanin uwa ta ne. To na kira kira gayya zuwa cikin daji.”
Bagudu na wannan jawabi ne a gaban dandazon jama’ar da su ka haɗa har da mafarauta da ‘yan tauri.
“An nuno shi tsakiyar wasu gwamnoni da su ka je domin yi masa jaje, cikin su har da Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi.
PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin yadda ‘yan bindiga su ka gudu da ɗalibai sama da 100. Kuma ta bada labarin yadda jami’an tsaro su ka kashe wasu ‘yan bindiga da dama, su ka ceto wasu ɗaliban.
Haka kuma wannan jarida ta yi bayanin yadda ‘yan bindiga ka neman hana yara karatun boko a Arewa.
‘Ta bada labarin ‘yan bindiga sun sake darkakar ɗaya daga cikin makarantun sakandare su ka kwashi ɗaliban da ba a bayyana adadin su ba a jihar Kebbi.
A wannan karo sun dira Kwalejin Gwamnatin Tarayya, ta garin Yauri su ka kwashi ɗalibai da malaman makaranta.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa an kwashi ɗaliban amma ba ta bayyana adadin su ba.
Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Jihar Kebbi, Nafiu Abubakar ya shaida a wata sanarwar da ya aiko wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan sanda masu gadin makarantar sun yi artabu da maharan har aka harbe jami’i ɗaya.
Ya ce a kan babura su ka darkaki Yauri, amma daga cikin dajin Rijau na Jihar Neja su ka fito, kuma a can su ka nausa da ɗaliban da su ka kwashe.
Rahotanni a wasu kafafen yaɗa labarai sun tabbatar da cewa duk da cewa ‘yan bindigar a babura su ka kai harin, sun kwashi wasu ɗaliban a cikin mota.
‘Yan sanda sun tabbatar wa iyayen yaran da cewa su ka cikin daji su ka farautar ‘yan bindigar.
Satar Ɗalibai: Yadda Karatun Boko Ke Neman Gagarar ‘Ya’yan Talakawa:
Kamar yadda Boko Haram su ka riƙa sace ɗaruruwan ɗalibai a baya, su ka ‘yan bindiga sun bi sawun su wajen yawan kwasar ɗalibai ana yin garkuwa da su.
A cikin 2021 an kai farmaki a makarantun sakandare da su ka haɗa da Jihar Katsina da aka kwashi ɗaruruwan ɗalibai a Ƙanƙara, sai Jihar Zamfara da Jihar Neja inda aka kwashi ɗalibai a garuruwa uku. A Katsina ma an saci ɗaliban Islamiyya 400 kan hanyar komawar su gida tsakar dare daga taron Maulidi.
A lokacin da aka kwashi ɗalibai na baya bayan nan a Kebbi, wasu ‘yan bindiga na riƙe da ɗaliban Islamiyya 139 na Tegina a Jihar Neja.
Sannan jihar Kaduna ta sha fama ita ma da kwashe ɗalibai tun daga na jami’a har zuwa na babbar kwaleji.
Sannan idan ba a manta ba dai a cikin wannan shekarar ‘yan bindiga sun kai samame a Kwalejin Turkish Collage da ke Kaduna, amma sojoji su ka fatsttake su.
Yanzu haka akwai wasu ɗaliban Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke hannun ‘yan bindiga. Kuma makarantar da ke Zariya ta kasance a rufe.
Yayin da ba a san adadin yawan ɗaliban Yauri da aka kwashe ba, haka nan kuma ba a san ranar da za a sako su ba. Duk kuwa ya yawan alwashin da jami’an tsaro ke sha cewa su na farautar maharan.