GARDAMAR KWALLON KAFA: Ɗan giya ya kashe ɗan Arsenal

0

Wani da aka tabbatar ya sha giya ya yi mankas, ya luma wa mai goyon bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal fasasshiyar kwalba, ya sheƙa shi lahira.

Lamarin ya faru a kan babban titin Lagos zuwa Badagary, daidai wurin masu saida jarida a tashar shiga da sauka mota ta Vox Bus Stop.

Inda aka yi kisan dai dama wuri ne da ake sayar da jarida, wanda jama’a ke taruwa ana tsayuwa cirko-cirko, ana gardandami kan baturuwan siyasa, tattalin arziki, ƙwallo da kuma duk wani hali da ƙasa ke ciki.

Wanda aka yi kisan a gaban sa ya shaida wa wakilin mu da ya je wurin bayan an tafi da wanda aka caka wa kwalbar asibiti, ya ce wanda aka burma wa kwallar ya mutu sunan sa Vigo.

“Gardama ta kacame tsakanin Vigo da ɗan giya, a kan wasan da ƙungiyar Arsenal ta London ta caskara ƙungiyar West Bromwich Albions da ci 5.

“Wannan ɗan giya da ya fusata, sai ya rarumo kwalba, kuma ya fasa ta, ya luma wa Vigo mai goyon bayan Arsenal a wuya.”

Majiyar ta ci gaba da cewa an garzaya da shi asibitin kuɗi, inda ana zuwa likitoci su ka tabbatar da cewa ya mutu.

“Yayin da mutanen da su ka kai shi asibiti su ka dawo wajen mai sayar da jarida, su ka samu ɗan giyar, sai su ka rufe shi da duka da falankan katako da sanduna.

“An yi masa laga-laga, kamar ba zai rayu ba. To kuma dama ana jin haushin sa ya taɓa kashe wani mai suna Baba Ijebu a wurin. Jama’a kuma na jin haushin ‘yan sanda ba su kama shi ba.

“Ko wannan dukan ma ai ‘yan sanda sun ga ana dukan sa, amma ba su yi magana ba. Sai da su ka ga za a rataya masa taya a ƙone shi, sannan su ka je su ka ɗauke shi a cikin wata mota ‘bas’, su ka yi gaba da shi.”

PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Legas, Adekunle Ajisebutu, amma ya ce ‘yan sandan Ojo Division da su ka ɗauki ɗan giyar, ba su bayar da rahoton komai ba tukunna.

Ya yi alƙawarin zai sanar da wakilin mu yadda ake ciki da zaran ya samu rahoton daga Ofishin ‘Yan Sanda na Ojo.

Share.

game da Author