Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed, ya kare dalili tare da bayar da hujjojin da su ka sa Shugaba Muhammadu Buhari ke fita Ingila ganin likita, duk kuwa da halin matsalar fannin kiwon lafiyar ƙasar nan ke fama da ita.
Lai ya yi wannan bayani a Washington, babban birnin Amurka, inda ya je domin ganawa da manyan kafafen yaɗa labarai.
Ministan ya je ne domin tallata masu ayyukan ci gaban da Gwamnatin Buhari ta samar a Najeriya.
Sannan kuma ya yi masu cikakken bayanin irin nasarorin da aka samu wajen ƙoƙarin daƙile ta’addanci, masu garkuwa da mutane da kuma mahara su kwasar dukiyoyin jama’a.
“Buhari na da ƴancin ya fita neman magani ko ganin likita. Domin ba shi ne Shugaban Ƙasa na farko a Najeriya da ya riƙa fita waje ganin likita ba.
“Kuma Buhari ya na da likitan sa a waje, wanda ke duba shi, ya san ciwon sa, ya san maganin sa da kuma tsarin jiyyar sa. Saboda haka don me za a ce sai ya saki likitan sa na tsawon shekaru 30 ya kama sabo daban?
“Ko a matsayi na na Minista, idan a baya ina da likitan da ya san ciwo na kuma na fi yarda da shi, babu dalilin da zai sa a matsa min lamba sai na sake likita don na zama minista.”
A kan haka Lai ya ce ko ɗan wace ƙasa ce likitan da ya fi fahimtar ciwon mutum, to ya na da ‘yancin riƙe shi a matsayin likitan sa.
Sannan kuma ya nuna cewa fitar da Buhari ke yi ba hujja ce da wasu ke cewa harkar kiwon lafiya a Najeriya ta durƙushe ba.
Cikin gidajen jaridun da Lai ya gana da su, har da BBC Radio da Talbijin, Bloomberg da kuma Politico.
Sannan kuma ya gana da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, a ofishin sa da ke Washington.