A kasar Ghana ne wani faston cocin Angilika ya rika sumbatar ‘yan mata a baki a daidai ana gudanar da ibada a coci.
Wannan abin mamaki ya auku ranar Lahadin da ta gabata a cocin Angilika dake kolejin koyar da malunta na ‘St. Monica’ dake Ashanti.
A bidiyon da aka saka a shafin tiwita da wasu shafukan sada zumunta a yanar gizo an ga sauran mutanen cocin na ta ihu a lokacin da wannan fasto ke sumbatar waɗannan ‘yan mata ko kunya baya ji.
A cewar fanston mai suna Obeng Larbi ya ce yana sumbatar ‘yan mata a cocin sa ne saboda nuna godiyarsa da kuma a madadin cocin bisa kokari da taimakawa ayyukan ibada da suke yi.
Da aka tattauna da daya daga cikin ‘yan matan da faston ya sumba ta ta bayyana wa Star FM cewa daya daga cikinsu ne ta saka bidiyon abin da ya faru a yanar gizo saboda basu ji daɗin abin da faston ya yi ba.
“Da farko ya sumbaci shugaban kungiyar masu binciken littafi mai Tsarki sannan da wasu ‘yan mata dake kungiyar mu.
A karshe mahukuntar wannan coci sun nuna bacin ran su kannabin da Fasto ya yi sannan za a hukunta shi kan abinda ya aikata.
Sannan za su tausa ƴan matan kada hakan ya canja musu ra’ayi game da cocin.
Discussion about this post