Wata ‘yar fim ɗin Nollywood mai suna Chioma Ifimeludike, ta fallasa lalatar da ta ce ya yi ita da Fasto Johnson Suleman.
Suleman shi ne Shugaban Cocin ‘Omega Fire Ministries Worldwide’.
Chioma ta yi wannan bayani ne a shafin ta na Instagram a ranar Asabar, a cikin wani bidiyo da kuma a rubuce da ta watsa a shafin.
A cikin bayanan na ta, ta ce dukkan lalatar da ta yi da Fasto Johnson Suleman, an biya ta kuɗin ta cas.
Ta ce ƙawar ta ce kuma ‘yar fim Lynda Clems ta yi mata kawalci, ta haɗa ta da Fasfo Suleman.
“Lynda, a yau dai na kasa daurewa, na fito na shaida wa duniya gaskiya cewa kin taɓa yi min kawalci, ki ka haɗa ni da Fasto John Suleman, a ranar 20 Ga Nuwamba, 2016 ya yi lalata da ni a otal a Ikeja, Lagos.
“Daga nan ya ba ni lambar sa a asirce. Sai wata rana kuma ya kira ni, na same shi a Oriental Hotels a Legas ɗin dai. Mu ka sake yin lalata, ya biya ni.”
Chioma ta ci gaba da cewa wannan abu daga baya ya riƙa damun ta, wanda a yanzu ya kai ta ga tuba a wurin Ubangiji.
“Ya kamata ke ma Lynda ki fito ki faɗa wa duniya gaskiya. Ni dai abin ya riƙa damu na. Ga shi na kasa daurewa, har na bayyana duniya ta sani.
“Ina roƙon jama’a su taya ni addu’ar tuba ga Ubangiji.
“A duk lokacin da na kalli Fasto Johnson Suleman na wa’azi a talabijin, sai rai na ya ɓaci na riƙa da-na-sani. Hakan kuma na tuna min cewa dukkan rigingimun da ya shiga a baya na zargin lalata da mata, to akwai ƙamshin gaskiya a lamarin kenan. Kuma na san ba za a rasa waɗanda ke tsoron fitowa su bayyana lalatar da su ka yi da faston ba.” Inji Chioma.
Ita dai Lynda ta mayar mata da martanin barazanar maka ta kotu. Ko da ya ke dai ta goge barazanar da ta yi wa ƙawar ta Chioma ɗin.
Wannan ne dai karo na uku da mata ke fitowa su na bayyana holewar da su ka riƙa yi da Fasto Johnson Suleman, wanda ke nuna ya fi kowa tsoron Ubangiji.