Hukumar EFCC ta damke tsohon gwamnan jihar Abia da dansa a filin jirgin sama an Nnamdi Azikwe, Abuja.
Dama kuma ba tun yanzu ba hukumar ke fakon sa ana ta bibiyar sa a dalilin bincike da ake yi a kansa na harkallar biliyoyin naira kudaden jihar da yayi ‘WUF’ dasu a lokacin da yake gwamnan jihar.
Da shi gwamnan da babban dan sa Chinedu Orji wanda shine kakakin majalisar jihar a yanzu na tsare a ofishin hukumar EFCC a Abuja ana gurza su kan harkallar da suka tafka.
Ana tuhumar Theodore Orji da dan sa Chinedu kan harkallar kudaden jihar, sama da fadi da kudaden jihar da sauran su.
An gano cewa sanata orji yana wawushe naira miliyan 500 duk wata daga rumbun kudaden tsaro na jihar, yana karkatar da su zuwa wata asusun musamman har tsawon shekara 8 da yayi yana mulki a jihar sa.
Bayan haka akwai wasu naira bilyan 2 da ya karkatar zuwa asusun bankin sa wanda kudaden gidauniyar kare zaizayar kasa da na tallafi ga marasa karfi, gaba daya ya wawushe su.
A takaice dai EFCC tana tuhumar Orji kan harkallar kudaden jihar Abia da suka kai rabin naira Tiriliya 1 da suka bace bat a lokacin yana mulki a jihar.