Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin Jama’a (NHRC), Tony Ojukwu, ya bayyana matuƙar ɓacin ran sa, ganin irin yawan waɗanda ke garƙame a kurkuku saboda ƙananan laifukan da ba su taka kara su ka karya ba.
Ya ƙara da cewa wasu dokokin musamman an tanade su ne kawai a kan talakan da ba shi da cin yau da na gobe da ya aikata ƙananan laifuka.
Ojukwu ya nuna wannan damuwar a wani taron tattauna yadda ake nuna wa marasa ƙarfin cikin al’umma bambanci wajen kafa dokoki a Afrika.
“Wato dokokin da ake ƙaƙabawa a kan masu ƙaramin ƙarfi su na kassara su tare da ƙara jefa su cikin ƙuncin rayuwar taɓarɓarewar tattalin arzikin su. Kuma dokokin su na maida waɗannan talakawa saniyar-ware” Inji Ojukwu.
Duk da Tony Ojukwu bai bayar da adadi ko ƙiyasin waɗanda ke tsare ɗin saboda ƙananan laifuka ba, amma dai ya nanata cewa waɗanda ake tsare da su a kurkuku, saboda ƙananan laifuka su ne su ka fi yawa. Kuma mafi yawan su duk jiran a yanke masu hukunci su ke yi.
“Abin takaici da tayar da hankali ne matuƙa ganin mafiya yawan waɗanda ke tsare a kurkuku duk marasa galihu ne da ke jiran a yanke masu hukunci tsawon lokaci ba a yanke masu ba.
“Laifin wani bai wuce wai ya yi wa wani babba rashin kunya ko tsaurin-ido ba, wasu a yawon gallafiri aka kama su, ba tare da sun ɗauki kayan kowa ba. Wasu zaune su ke wurin hira aka rarume su aka garƙame. Wasu an kulle su wai don su na yawon bara. Wasu talla, wasu bashi su ka kasa biya, sai aka yi masu bi-ta-da-ƙullin garƙame shi a kurkuku. Wasu ma an kulle su saboda kawai masu hali ba sa son jin hayaniyar su a cikin kunnuwan su.”
Ojukwu ya ce waɗanda ake yi wa irin wannan kamun a kan titina, an fi yin sa a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Ya ce aikin kamfen ɗin daina ƙuntata wa talaka da tsauraran dokokin kassara shi, ya ɗauki harama ne tare da haɗin kan NHRC da kuma cibiyar NANHRI ta Afrika.