DOKAR BUNƘASA MAN FETUR: Sanata Lawan ya ƙaryata zargin cika masa aljifai da dala miliyan 10 don ya baddala ƙudirorin doka

0

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan ya ƙaryata zargin da aka yi masa cewa an ba shi cin hancin dala miliyan 10 don ya baddala ƙudirorin dokar raba ribar man fetur, wadda ya gaggauta sa wa hannu ta zama doka.

Lawan ya ce ko shi ko Shugaban Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ko ma wani Sanata ko Mamba, babu wanda ya karɓi waɗannan maƙudan kuɗaɗe.

Sanata Lawan ya yi wannan bayani ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, jim kaɗan bayan ganawar sa da Shugaba Muhammadu Buhari.

Lawal ya yi martanin ne bisa raddi kan wani zargi da ake cewa wasu ‘yan majalisa sun nuna jin haushin yadda Sanata Lawan ya karɓi rashawa har ta dala miliyan 10, ya bagaras da su, ya damalmala kudiroi dokar fetur (PIB), kafin ya damƙa wa Shugaba Buhari ya sa mata hannu ta zama doka.

Rahotanni sun ce an biya Lawan dala miliyan 10 domin ya sa hannun amincewa da biyan kashi 3% bisa 100% ga yankunan da ake haƙo ɗanyen mai a cikin su.

Lawan ya yi gargaɗin cewa jama’a na wuce gona da iri wajen furta duk abin da su ka ga dama da sunan faɗin ‘yancin albarkacin baki.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda aka riƙa dambarwa kan kashi 3% bisa 100%.

“Mutane su na kiran shugaban ƙasa da baƙaƙen kalamai, kamar yadda mu na sanatoci da mambobin majalisa su ke kiran su da kalamai na ɓatanci. Ai dimokraɗiyya ɗin kenan.”

Lawan ya ce ya na jaddada a daina kiran shugabanni da baƙaƙen kalamai.

Share.

game da Author