Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa za ta gudanar da gangamin taron ta na ƙasa a cikin watan Oktoba, domin zaɓen Sabbin Shugabannin Kwamitin Zartaswa.
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP, Aminu Tambuwal ne ya bayyana haka ga manema labarai, bayan fitowa daga taron ganawa da shugabannin jam’iyya a Abuja.
Ganawar wadda ta ɗauke su tsawon sa’o’i da dama, ta samu halartar gwamnonin PDP, Mambobin Kwamitin Amintattu da kuma ‘Yan Majalisar Tarayya.
Akwai kuma wasu daga tsoffin gwamnoni, tsoffin ministoci da manyan ‘yan jam’iyya duk sun hallara.
An dai haɗa taron ne domin a sasanta rikicin da ya tirniƙe jam’iyyar, wanda wasu ɓangarorin PDP ɗin su ka nemi Shugaban Jam’iyya Uche Secondus ya sauka daga muƙamin sa.
An dai zaɓi su Uche Secondus a cikin watan Disamba, 2017 domin riƙe jam’iyya tsawon shekaru huɗu.
Duk da cewa cikin watan Disamba mai zuwa ne ya kamata a yi taron gangamin sake zaɓen, rikicin ɗaya tirniƙe jam’iyyar ne ya tilasta shirya taron wanda za a yi tun cikin watan Oktoba.
Tambuwal ya ce kwamitin NEC zai gana domin kafa kwamitin da zai rattaba shiyyoyin da shugabannin jam’iyyar za su fito a lokacin zaɓe.
Bayan taron dai an roƙi dukkan masu sa-in-sa su haƙura, kowa ya maida wuƙar sa a cikin kube.
PREMIUM TIMES ta buga labarin dambarwar neman tunkuɗe shugaban PDP kan mulki, inda shi kuma ya ce ba zai sauka daga shugabancin PDP ba, tunda bai aikata laifin komai ba.
Shugaban Jam’iyyar PDP mai fuskantar matsin-lamba, Uche Secondus, ya bayyana cewa ba zai sauka daga shugabancin PDP ba, tunda bai aikata laifin komai ba.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran Secondus, mai suna Ike Abonyi ya fitar, ta ce duk wani mai tayar da jijiyar wuyar neman Secondus ya sauka, to ya fara fitowa da laifukan da ya yi kowa ya gani tukunna.
Sanarwar ta ce bai aikata wani laifin da za a ce ya cancanci saukewa ko wajibcin saukewa ba.
“Saboda haka wasu ‘yan tsirarun da ke cewa Secondus ya sauka, su fito su bayyana laifukan da ya aikata.
“Secondus ba zai suka ba, zai ci gaba da jagorantar PDP tare da yi mata kyakkyawan riƙon da ya yi rantsuwar zai ci gaba da yi mata, watanni 44 da su ka gabata da aka rantsar da shi.”
Wannan kakkausan jawabi yazo ne sa’o’i kaɗan bayan Mambobin Majalisar Tarayya na PDP sun nemi Secondus ya sauka daga shugabancin jam’iyyar.
Sun ce akwai hatsari nan gaba idan Secondus ya ci gaba da kasancewa shugaban PDP.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda lemar PDP ta kama da wuta, bayan wasu jiga-jigan jam’iyya takwas sun yi murabus, sun bar gwamnonin su da kururuwar neman gudummawar kashe gobara.
Kwana ɗaya bayan jiga-jigan jam’iyyar PDP su bakwai sun ajiye ayyukan su na shugabancin jam’iyya a matakai daban-daban na ƙasa, an samu tsohuwar Sanata Joy Emordi, ɗaya daga cikin Shugabannin Kwamitin Amintattun PDP ta koma jam’iyyar APC.
Sai dai kuma duk da wannan koma baya da PDP ta samu,gwamnonin jam’iyyar sun roƙi a kwantar da hankali kuma a kai zuciya nesa, za su kyara wa gobarar ruwa su kashe wutar.
Gwamnan Sokoto kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP, Aminu Tambuwal ne ya yi kiran a Abuja.
Yayin da ya ke jaddada cewa za su shawo kan lamarin, Tambuwal ya ce PDP ce jam’iyyar da ƙasar nan ta zura wa ido tare da fatan za ta saisaita damalmalawar da mulkin APC ya yi wa Najeriya.
Waɗanda Su Ka Ajiye Muƙaman Su:
Masu riƙe da muƙamin mataimaka a muƙamai bakwai ne su ka ajiye aikin su a ranar Talata, daga Babban Kwamitin Zartaswar PDP.
Akwai Mataimakin Sakataren Yaɗa Labaran PDP na Ƙasa, Diran Odeyemi; Mataimakin Mashawarci a Fannin Shari’a, Ahmed Bello; Mataimakiyar Shugabar Mata, Hadizat Umoru da kuma Mataimakiyar Mai Binciken Kuɗi, Divine Amina Arong.
Sai kuma Mataimakin Sakataren Tsare-tsare, Hassan Yakubu; Mataimakin Sakataren Kuɗi, Irona Alphonsus.
Dukkan su sun ce sun sauka ne saboda zargin su cewa Shugaban Jam’iyya Uche Secondus bai iya tafiyar da shugabancin jam’iyyar bisa yadda ya dace ba.
Ba Ni Na Cinna Wa Lemar PDP Wuta Ba -Atiku
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya yi watsi da surutan bayan fage da ake yi cewa shi ne ya ruruta wutar rikicin jam’iyyar PDP wanda ke neman zama gobarar jam’iyya a yanzu.
Atiku na ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP da ake nunawa da yatsa cewa su na ƙoƙarin tumɓuke Shugaban PDP na Ƙasa, Uche Secondus.
Atiku ya bayyana cewa shi ƙoƙarin tabbatar da haɗin kai da kuma ɗinke ɓaraka ya yi a cikin PDP, maimakon ruruta wutar rikicin da wasu ke cewa ya yi.
Ya ce ya goyi bayan sasantawa da kuma haɗin kan jam’iyyar PDP kamar yadda aka ga ya riƙa yi a baya-bayan nan.
Daga nan ya yi kira da kowa ya haƙura, a maidai takubba cikin kube, domin ci gaban PDP a ƙasa baki ɗaya.
Atiku ya ce bai kamata jam’iyyar adawa ta faɗa cikin rikici ba, a daidai lokacin da jam’iyya mai mulki ta kasa cika wa al’umma alƙawurra, kuma a lokacin da ‘yan Najeriya su ka gaji da mulkin ta.
Ya ce ya kamata a samu haɗin kai a PDP, domin a kawar da APC a zaɓen 2023.
“Duk masu son ci gaba da mulki ko da talakawan ƙasar nan ba su so ne ke ta ruruta wutar rikice-rikice a cikin PDP, don kada mulki ya suɓuce daga hannun sa idan zaɓen 2023 ya zo.”
Discussion about this post