Biloniyan attajiri Femi Otedola ya fito a ranar Lahadi ya na taya toshon Shugaban Ƙasa Ibrahim Babangida murnar cika shekaru 80 da haihuwa.
Babangida wanda ya yi mulki tsakanin 1985 zuwa 1993, zai cika shekaru 80 a duniya, ranar Talata, 17 Ga Agusta.
Otedola ya yi wannan bayani na sa ne a cikin wani littafin sa fitowa a cikin watan Nuwamba.
Ya ce lokacin da tsohon Shugaban Ƙasa Marigayi Umaru ‘Yar’Adua ba shi da lafiya, ya na ƙasar waje ya na jiyya, kuma an ƙi damƙa mulki a hannun Mataimakin sa Goodluck Jonathan, shi Otedola ɗin ne Babangida ya aika wajen Jonathan, ya ce masa idan an je Taron Majalisar Zartaswa, kada ya hau kujerar Mataimaki, ya zarce ya hau ta ‘Yar’Adua, wato ta Shugaban Ƙasa.
“Cikin 2010 mun je Minna domin yi wa Babangida murnar zagayowar ranar haihuwar. Mu ka zauna ana hirarraki da taɗi daban-daban. Can dai na ce masa ina so mu gana a keɓance da shi. Daga nan a ka kai ni keɓantaccen ɗakin da ya ke ganawar sirri.
“Na ce masa ranka ya daɗe ƙasar nan fa na cikin wani mummunan yanayin ƙadabolo ko cukumurɗa da dambarwar mulki, tunda dai ‘Yar’Adua ya tafi jiyya bai damƙa mulki ga Jonathan ba. IBB ya zura mani ido kawai. Da na gama magana, sai ya ce min to idan ka koma Abuja, ka je ka same shi ka ce masa na ce idan ya shiga Taron Majalisar Zartaswa mako mai zuwa, kada ya zauna a kan kujerar sa, ya zarce kai-tsaye ya zauna a kan ta ‘Yar’Adua.”
Da yamma a ranar na koma Abuja a mota ba ma a jirgi ba. Saboda zumuɗi Ni kuma sai na zarce kai-tsaye Fadar Shugaban Ƙasa. Bayan mun gama cin abincin dare, sai na isar masa da saƙo na. Bayan na gama magana, Jonathan ya ɗan ƙura min idanu. Can dai ya ce min to zai yi tunani.
To dama ranar Laraba ake yin taron. Sai ya kasance wasu abubuwa sun biyo baya. Kuma dama kafin sannan ana ta kicimillar wasu na so a damƙa shugabancin riƙo ga Jonathan, wasu kuma ba su so. Ranar Talata kafin zuwan Laraba ɗin, sai Majalisar Tarayya ta zartar da Dokar Dole, wadda ta wajabta wa Jonathan zama Shugaban Riƙo.
“Washegari ranar Laraba an je wajen Taron Majalisar Zartaswa, da Jonathan ya shiga ɗakin taro, sai babban hadimin sa ya fara gyara masa kujerar sa ta Mataimakin Shugaba domin ya zauna. Shi kuma sai ya wuce kujerar, ya zarce kawai ya haye ɗare-ɗare a kan ta ‘Yar’Adua, wato ta Shugaban Ƙasa.”
Otedola ya ce daga ranar ce Jonathan ya nuna shi fa namijin duniya ne. Kuma a ranar sai da ya yi sauye-sauyen Ministoci.
Hamshaƙin miloniyan ya ce ya bada wannan labarin ne domin ya zaburar da ‘yan kasuwa su riƙa jibintar ‘yan siyasa da gwamnati, ta yadda za su fi bayar da ta su gudummawa wajen gina ƙasa.
“Ni ma dalilin kusanci na da gwamnati ne har na samu damar bada wannan muhimmiyar gudummawa, a lokacin da ƙasar nan ke cikin halin tsaka-mai-wuya.” Inji Otedola.