Sakataren Jam’iyyar APC na Ƙasa, John Akpanudoedehe ya bayyana cewa an jibge jami’an tsaro a Hedikwatar APC da ke Abuja ranar Litinin ne domin ƙarfafa tsaro a ofishin na ƙasa.
Da ya ke ganawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin, Akpanudoedehe ya ce babu wani abin nuna damuwa ko tayar da hankali.
Ya ce zaratan ‘yan sandan da aka jibge a hedikwatar da ke kan titin Balantire Street, kusa da Barcelona Hotel a Wuse 2 Abuja, an yi kawai domin ƙarfafa tsaro.
“An ƙaro ‘yan sanda ne domin su ƙara wa shugabancin Gwamna Mai-Mala Buni ƙarfin tsaro.
“A duk lokacin da ka tsinkayi alamomin wata matsala ko rahoton wata barazar tsaro, to abu na farko shi ne ɗaukar matakin gaggawa.
“Ba za mu taɓa bari wasu ‘yan tsiraru sun kunyata mu ba, saboda mu ne ke riƙe da gwamnati a ƙasar nan. dalili kenan mu ka ɗauki matakan kariyar duk wata shegantakar da ka iya bijirowa.
“Mun samu rahoton sirri na jami’an tsaro. Don haka ba zai yiwu mu ɗauko ‘yan iska da ‘yan jagaliya su zo su kare Sakateriyar APC ta Ƙasa a Abuja ba. Abin da ya dace shi ne mu sanar wa ‘yan sanda da SSS. Kuma hakan mu ka yi.” Inji Akpanudoedehe.
Idan ba a manta ba ita ma APC ta shiga ruɗani, yayin da wasu jiga-jigan ta su ka nemi Shugaban Riƙo Gwamna Buni ya sauka, domin dokar ƙasa ba ta yarda Gwamna ya riƙe wani muƙami ba.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga rahoton da Karamin Ministan Ƙwadago, Festus Keyamo ya yi gargaɗin cewa mulki zai suɓuce daga hannun APC idan Gwamna Buni ya ci gaba da shugabancin jam’iyyar ko na tsawon sati ɗaya ne.
Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Festus Keyamo, ya gargaɗi jam’iyyar APC cewa akwai gagarimar matsalar da ta tunkari jam’iyyar, matsawar Gwamna Mai Mala-Buni na Jihar Yobe ya ci gaba da kasancewa Shugaban Jam’iyya na Riƙo har zuwa jibi Asabar, ranar zaɓe shugabannin APC a matakan Kananan Hukumomi da Jihohi da za’a yi ranar 31 Ga Yuli.
Yayin da ya aika da wata wasiƙar gaggawa ga jam’iyya s asirce, wadda ta faɗo hannun PREMIUM TIMES, Keyamo wanda shi ma gogaggen lauya ne, ya bayyana haramcin riƙe APC da Gwamna Buni ke yi, domin Dokar Ƙasa da Dokar APC sun haramta Gwamna ya riƙe wani muƙami ko shugabanci banda na gwamna da aka rantsar da shi don ya riƙe.
Wannan mahaukaciyar guguwa ta taso ne sanadiyyar hukuncin da Kotun Ƙoli ta Yanke, inda ta jaddada nasarar Gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo, na APC, kan Eyitayo Jegede na PDP.
Discussion about this post