Dalilin da ya sa masana’antun kifi ba su da tasiri a Najeriya – Wani masani

0

Wani tsohon malamin jami’a, ya bayyana dalilin da ya sa masana’antun kifi da kiwon kifi ba su yin tasiri a Najeriya.

Nalaguo Alagoa mai shekaru 69 a duniya, tsohon malamin jami’a ne a Jami’ar Jihar Ribas. Kaɗan daga cikin dalilan da ya lissafa sun haɗa da rashin maida hankalin gwamnati a harkar kifi da kuma gurɓacewar yanayi.

Tsohon malamin ya shafe shekaru da dama a jami’ar ya na koyar da dabarun kiwon kifi da sauran namun cikin ruwa.

A tattaunawar da ya yi da wakilin mu, ya bayyana cewa ba daidai ba ne da ake cewa masu sana’ar kifi su da manoma matalauta ne.

“Misali, ba gaskiya ba ne da ake cewa jihohin Ribas da Bayelsa sun fi sauran jihohi kifi a Najeriya.

“Jihar Legas ta fi su kifaye, amma an fi yin kamun kifi a jihohin Ribas, Bayelsa, Cross Rivers da sauran su.”

“To kuma mu na fama da babbar matsalar gurɓacewar muhalli. Yanzu waɗannan wurare duk ba su samar da kifi kasar yadda su ke samarwa a shekarun baya.

“Abu na biyu kuma akwai matsalar ambaliyar da Kogin Neja ya yi cikin 2012, wadda shekaru masu yawa a baya ba mu taɓa ganin irin wannan ambaliyar ba.

“Abin da ya haifar da wannan ambaliyar kuwa shi ne aikin madatsar ruwa Neja da Kaiji.

“Sakacin matasan mu na nan yankin Neja Delta da su ka yi watsi da kamun kifi, ya sa matasa daga Arewa na kwararo mana a nan su na neman ƙwace sana’ar kamun kifi. Su kuma matasan mu sun bar gida su shiga duniya neman aikin samun kuɗi ana kwance ko zaune a ofis ana shan sanyi.

“Yanzu haka idan za ka bi ka binciki masuntan mu na yankin Neja Delta, za ka ga duk dattawa ne daga shekaru 60 abin da ya yi sama. Duk matasan mu sun yi watsi da wannan sana’a, sun shiga cikin duniya neman aikin da babu tabbas su samu.

“Sai kuma matayen yankin mu masu kamun kifi domin samun ‘yan kuɗin rufa wa kai asiri, saboda sun rasa mazajen su. Sai kuma iyayen da ba su da ‘ya’yan da za su riƙa ɗaukar ɗawainiyar kulawa da su. Su ne ke saida rayukan su su na wannan sana’a mai cike da haɗari a rayukan su.” Inji shi.

“A yanzu idan ka fita kamun kifin ma ba lallai ba ne ka koma da abin kirki a gida. Sai ka yini ka koma gida da ɗan kaɗan, sai ka sake komawa washegari ka meni dacewa. Amma a shekarun baya ba haka abin ya ke ba.

“Babban dalilin da ya haifar da haka kuwa shi ne gurɓacewar yanayi. Wannan kuma ba daga laifin mazaunan yankin ba ne. Daga gwamnati ne da ta ke bijiro da tsare-tsaren da ke haifar da gurɓatar yanayin mu a nan.

“Ta kai yanzu baƙi ne ke zuwa su yi harkokin kamun kifi, su sayar, sannan su kwashi kuɗaɗen su su koma jihohin su. Ko haraji ba su biya, a nan dai jihar Bayelsa.

“Idan ka bi gefen teku ka na tafiya, mataccen kifi kawai za ka riƙa gani a bakin ruwa, ko waɗanda ke magagin mutuwa a gefen ruwan teku da ke Jihar Bayelsa. Hukumar NOSDRA da ya kamata a ce ta yi wani yunƙuri a cikin gaggawa, har yau ba ta sanar da mu dalilin da ya sa kifaye ke mutuwa a Neja Delta ba.”

Ko a shekarun baya ma mun sha ganin jiragen ruwan Chana da Japan su na kamun kifi a ruwan yankin Bayelsa. Sai su tara kifaye da yawa, su kwashe su kai Legas su sayar, a matsayin kifayen da aka shigo da su daga ƙasashen waje. Alhali kuma na mu ne nan na cikin ruwan Najeriya.” Inji tsohon malamin jami’ar.

Share.

game da Author