Dalilin da ya sa Gwamnatin Katsina za ta riƙa karɓar haraji da jangalin naira 2,000

0

Shugaban Hukumar Tara Kuɗaɗen Harajin Jihar Katsina, Mustapha Suraj, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa lokacin da ya zama shugaban hukumar ya fuskanci ƙalubale musamman ɓarkewar cutar korona, kulle mutane a gida da kuma hana fita a yi kasuwanci.

Lamarin wanda ya ce har fannin cinikin ɗanyen mai sai da matsalar ta shafa a duniya baki ɗaya.

“Amma yanzu a hankali komai ya fara warwarewa. A watan jiya mun tara kuɗin haraji za su kai naira miliyan 700. Amma a baya ba a samun irin wannan adadin.

“Kamar yadda ka ce jihohi irin su Katsina, Kano da Kaduna ba su taɓukawa sosai batun tara kuɗaɗen haraji, a Katsina mu na bakin ƙoƙarin mu. Amma fa ka san ba za mu iya kamo wasu jihohi musamman irin su Lagos da jihohin da ke da arzikin fetur ba.

“Sai dai mu na da tsari da zai kai mu ga zarce irin su Jihar Kaduna wajen tara kuɗaɗen haraji.”

Ya ce tun farkon hawan sa shugabanci ya riƙa samar da horo ga ma’aikatan da ke a ƙarƙashin sa. An yi masu horo har iri daban-daban guda shida.

“Na zo da kuzarin yin aiki tuƙuru, kuma na tabbatar haka su ma Hukumar Gudanarwar ofishin ke ci gaba da yi. To amma kuma ka san idan ka tsara abu, ba a rana ɗaya abin da ka tsara zai tabbata ba. Sai ya ɗan ɗauki lokaci.

Batun Jangali Da Harajin Naira 2,000 Da Za A Riƙa Karɓa A Katsina:

“Duk da ƙorafe-ƙorafen da ake yi, musamman daga waɗanda ba su da aikin yi, amma ni ina ganin ɗora wa mutum harajin naira 2,000 a shekara ba wani abin damuwa ba ne. Domin za a tara kuɗaɗen ne domin tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar Katsina.

“Sai mu tsaya mu kalli halin da mu ka shiga har aka yi tunanin ƙirƙiro harajin. Sannan kuma idan ka raba kudin zuwa wata-wata, za ka ga cewa ba su ma kai naira 170 duk wata ba. Saboda haka jama’a za su iya biya.

Da wakilin mu ya tambaye shi cewa akwai fa ɗimbin mutanen da ba su ma iya samun abinci su ci sau uku a rana, sai Suraj ya ce, “ai ba rana tsaka haka kawai aka wayi gari Gwamna ya kafa dokar ba. Sai da aka kafa kwamiti ya bi dukkan ƙananan hukumomi 34 ya ji ra’ayoyin jama’a tukunna.”

Da aka tambaye shi babu wata hanyar tara kuɗaɗen har sai an ƙaƙaba wa masu ƙarfi da marasa galihu haraji da jangali, sai ya ce ai ba yanzu ne aka fara jangali da haraji ba.

Daga nan ya ce wasu lokutan mutane ba su cika don bin doka ba.

Ya ce idan a Jamhuriyar Nijar ce, babu wani kwamitin jin ra’ayin jama’a da za a bi a saurara, sai dai a wayi gari a ji an kafa sabuwar doka kawai.”

Daga nan kuma shugaban na hukumar tara kuɗaɗen haraji a Jihar Katsina, ya ci gaba da bayyana irin nasarorin da ya sanar a ƙarƙashin shugabancin sa da bai kai cikakkar shekara ɗaya a kan kujerar ba.

Share.

game da Author