Kwamishinan kiwon lafiyar jihar Barno Juliana Bitrus ta bayyana cewa cutar Amai da Gudawa ta yi ajalin mutum 43 sannan mutum 559 sun kamu a jihar.
A taron da ta yi da manema labarai a garin Maiduguri Juliana ta ce cutar ta bullo a kananan hukumomin Gwoza, Kaga, Hawul, Magumeri, Dambao, Maiduguri Metropolitan da Jere.
Ta ce mutum 354 sun kamu, mutum 18 sun mutu a karamar hukumar Gwoza, mutum 126 sun kamu, mutum 11 sun mutu a Hawul.
A karamar hukumar Kafa mutum 2 sun mutu, mutum 22 sun kamu, Magumeri ta samu mutum 6 da suka kamu kuma mutum 1 ya mutu.
Mutum 39 sun kamu, mutum 10 sun mutu a Damboa sannan a Jere mutum 4 ne suka kamu babu wanda aka rasa.
Juliana ta ce cutar bata bullo ba a shekaran 2019 da 2020 ba a jihar.
Matakan dakile yaduwar cutar da gwamnati ta dauka
Juliana ta ce gwamnati ta dauki ma’aikatan lafiyan da za su gudanar da bincike domin gano wadanda suka kamu da cutar domin samar musu da kula cikin gaggawa.
Gwamnati ta kuma bude asibitoci domin kula da masu fama da cutar a kananan hukumomin da cutar ta barke.
Sannan duk manya-manyan asibitocin dake jihar sun kebe wuri domin kula da masu fama da cutar.
A karshe kwamishinar ta yi kira ga mutane da su rika tsaftace muhallin su sannan su rika kula da abincin da suke ci.
Discussion about this post