Hada-hadar ‘Bitcoin’ da aka shafe shekaru 10 ana cin kasuwar sa a duniya, kuma a zamanance, wani tsari ne a ajiyar kuɗin ka da sunan sayen kadara ta ƙwandalar ‘bitcoin’, yadda a kwana a tashi darajar ta ke ƙaruwa, tamkar dai ajiyar sarƙoƙin gwala-gwalai da farashin su ke tashi akai-akai, ko bagatatan.
‘Cryptocurrency’ babban bajau ne da na duniya, amma ba na caca ba. Sai dai kuma kamar ɗan cacar, akan wayi gari shi ma ɗan hada-hadar ‘bitcoin’ ya kuɗance cikin minti ɗaya. Kuma a kan samu akasi, darajar ƙwandalar ‘bitcoin’ ta karye, ka wayi gari ko ɓeran masallaci bai kai ka talauci ba, saboda ɗibga a asara a cikin minti ɗaya.
‘Cryptocurrency’ ba damfara ba ce, ba wala-wala ba ce, kuma ba kalo-kalo ba ce.
Hada-hada ce a kan bajau ɗin da mutum kusan miliyan 346 ke hada-hada a kan sa a duniya.
Babu wanda ya san babban kartagin wannan kasuwanci. Amma dai sunan sa Satoshi Nakamoto, sunan da duk duniya ba a san ko wa ke da shi ba. Sunan gare ne, amma kuma masu cinikin biri a sama sun yi amanna da shi. Saboda a kan bajau ɗin sa babu ƙwange, babu rinto, kuma babu damfara. Ko dai ka ci riba, ko kuma ka faɗi.
Akasari ba kasuwanci ne da mutum zai ƙunduge jarin sa kankat ya naka ba. Saboda komai na iya kasancewa.
Cinikin Kasadar Matasan Arewa
Daga cikin amfanin ‘bitcoin’, za ka iya amfani da kuɗin ka yi hada-hadar wani kasuwancin ba tare da ka sha wahalar jeƙala-jeƙalar bankuna ko wasu cibiyoyin kasuwanci ba.
Labaran Balarabe ya gama jami’a shekaru huɗu da su ka gabata, kuma ya nemi aiki har Abuja ya gaji bai samu ba.
A cikin ruguguwar lamunin noma bayan korona, Labaran ya cika fam ya samu ramce. Maimakon ya maka kuɗin a gona, bayan wani lokaci sai ga shi ya yi aure, ya kama hanyar gida mai tsada, kuma ya sayi shimfiɗeɗiyar mota, ya na ketawa duk inda ya ke so.
Duk inda ya shiga ake labarin sa, sai ka ji ana cewa ”Ai ɗan Bitcoin ne.”
Harkar Bitcoin kasada ce. Amma akwai samu, tamkar da aljanu mutum ke mu’amala su ka yi masa ruwan kuɗi.
Akwai lokacin da ƙwandalar ‘bitcoin’ ta ke duk guda ɗaya dala $150. Amma a cikin Afrilu, 2021, sai da guda ɗaya ya haura $64,000, daga nan kuma ta yi faɗuwar-‘yan-bori ƙasa warwas.
Sai dai kuma a ranar Litinin ɗin nan, ƙwandalar Bitcoin ta sake tashi sama har ta ɗan haura $50,000.
Abin mamaki, ƙasashen Amurka da Najeriya ne aka fi amfani da hada-hadar Cyrptocurrency ta Bitcoin. Ƙoƙarin da Babban Bankin Najeriya ke yi na haramta kasuwancin bai yi tasiri sosai ba. Saboda akwai kasuwancin tsaye da miliyoyin dalolin da CBN bai ma san ana yi ba.
Masu Hada-hadar Bitcoin su na amfani ne da wata manhajar bajau ta ‘digital’, wadda ake tura wa mutum lambar sirri ‘code’ mai sarƙaƙiyar da babu yadda za a yi wani ya yi maka kutsen gano lambar sirrin ka.
Ko shakka babu wannan hada-hadar sayen kadarar ƙwandalar Bitcoin ya mamaye Arewa. Ko dai ka zuba kuɗin ka a kan bajau ka kwashi riba mai yawan gasken da ta fi uwar kuɗin ka yawa, ko kuma ka yi asarar da washegari idan babu komai aljihun ka, to na shan kiki da ƙosai da safe ma su gagare ka.
Discussion about this post