CIKIN SHEKARU SHIDA: Yadda Buhari ya shafe fiye da kwanaki 200 wurin ganin likita a Landan

0

Shugaba Muhammadu Buhari na a cikin sahun gaban waɗanda su ka riƙa yin kiraye-kirayen Shugaba Umaru Musa ‘Yar’Adua ya sauka daga mulki, a lokacin da aka kwantar da shi asibiti a ƙasar Saudiyya. Sun riƙa ƙoƙarin rashin ingantattun asibitoci a cikin Najeriya.

Sai dai kuma yayin da Buhari ya hau mulki cikin 2015, bai daɗe a kan mulki ba shi ma ya fara zirga-zirgar ganin likitocin sa a Landan. Daga hawan sa mulki zuwa ƙarshen watan Yuli 2021, Buhari ya kwashe kwanaki fiye da 200 a Landan wajen ganin likitocin sa.

Ko Buhari zai gina asibitin da Shugaban Ƙasa zai iya tuntuɓa idan ƙaramar lalura ta dame shi? Ko kuwa haka za a ci gaba da tafiya, duk shugaban da ya hau ya riƙa fita neman magani a waje, su kuma asibitocin ƙasar nan babu wata ƙwarewa sai ƙwarewar yi wa marasa lafiya yajin aiki?na ‘yan dabaru.

Share.

game da Author