Wani jan aiki na gina jiha tun daga tushe, wacce ta ke daga yanayi na faƙo da duwarwatsu, zuwa garuruwa da suka zama maraya, da ake ganin kamar ba zai yiwu ba, sai ga shi ta ya tabbata. A halin yanzu, Jihar Jigawa ta hau kan wani ƙadami na ci gaba, wanda hakan ya samu ne sakamakon hoɓɓasar da gwamnoninta su ka yi, musamman Sule Lamiɗo da Badaru Abubakar.
Ƙirƙirar Jihar Jigawa a ranar 27 ga watan Agusta, 1991, da Shugaban Kasa Ibrahim Badamasi Babangida ya yi, ya kuma sanya babban birnin jihar ya kasance a Dutse ya girgiza al’ummar jihar da ma ƙasa baki ɗaya. Sannan matakin ya haifar da ɓacin rai ga al’ummar jihar.
Idan ka tattara irin ayyukan da gwamnonin baya su ka yi, tun daga kan Kanal Olayinka Sule, Ali Sa’ad Birninkudu, Birgediya-Janar Ibrahim Aliyu, Kanal Rasheed Shekoni, Laftanal-Kanal Abubakar Zakari Maimalari zuwa Ibrahim Saminu Turaki, Jigawa ba ta isa ta bigi ƙirji ta ce ta samu ci gaba ba.
Sule Lamiɗo ya gaji jiha wacce take ta noma ce amma kuma ta samu koma baya wajen tattalin arziki, ilimi, sannan kan al’ummarta a rarrabe ya ke. Kai, a ko wanne matsayi na ci gaba, an bar Jigawa a baya.
A zangonshi na farko a matsayin gwamna, Lamiɗo ya fi maida hankali a kan bunƙasa ilimi, in da ya gina sama da ajujuwa 1,000 kuma dukkansu da bencinan zama a faɗin jihar. Ya kuma samar da ƙananan makarantun gaba da firamare 21 gami da makarantun makiyaya har 216 a faɗin jihar, har ma ya samar da Jami’a.
Haka nan kuma Lamiɗo ya samar da bunƙasar gine-gine da dama da ma sauran abubuwan more rayuwa domin ya ɗora jihar a kan gwadabe na ci gaba.
A lokacin da aka rantsar da Muhammad Abubakar Badaru a matsayin Gwamnan Jihar Jigawa a shekara ta 2015, ya gabatar da wani jawabi mai cike da hikima da ya baiwa al’ummar Jihar tabbacin cewa Gwamnan zai kai su ga tudun-mun-tsira.
A watan Afrilu na 2015, Badaru ya ce “Tushen mulkin da za mu aiwatar zai ba da karfi ne a kan tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma, samar da ingantacciyar rayuwa ga jama’a, ruwan sha, ingantaccen kiwon lafiya, sama wa matasa aikin yi, sama wa mata sana’o’i da kuma yaki da talauci ta hanyar inganta aikin noma da kiwo”.
Bisa wannan jawabi da Badaru ya yi, ya kasance daya daga cikin gwamnoni kalilan a Nijeriya da suka yi fice wajen dora jihohin su bisa tafarkin ci gaban zamani na karni na 21.
Irin manyan ayyuka da Gwamna Badaru ya ke kan gudanarwa a jihar sa sun burge mai girma Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, lokacin da aka gayyace shi kaddamar da wasu daga cikin su saboda yawan su da kuma ingancin su a ranar 1 ga watan Yuli.
A cikin shekaru shida kawai, wannan gwamnan ya biya bukatun al’ummarsa ta wannan jaririyar jihar, inda ya sama masu ci gaban da har suna ganin daidai suke da sauran sa’annin jihohi da ke Arewaci da ma Yammacin kasar nan.
Nazarin da duk mai karatun wannan rubutu zai yi na shekaru shida masu albarka da Badaru ya yi a matsayin gwamna zai sa ya fahimci cewa ba karamin aiki ya yi ba wurin sama wa Jihar Jigawa ci gaba. Tun daga harkar ilimi, samar da lafiya, hanyoyi, aikin noma, sashen ma’aikatar gwamnati da sauran sassa, Gwamna Badaru ya samu manyan nasarorin da samun sama da su abu ne da kamar wuya.
Abu na farko da ya aiwatar bayan ya hau karagar mulki shine inganta hanyoyin samar da kudaden shiga na jihar, wadanda da su ya yi amfani wurin aiwatar da manyan ayyukan da ya yi a jihar.
A lokacin da ya hau mulki, Badaru ya tarar da kudin shigar jihar a kan matakin N2,343,974,525.10 a shekara ta 2015, wanda ya zuwa shekara ta 2019 kudin ya bunkasa, inda jihar take samun N8,537,371,114.59.
A sashen ma’aikatan jihar, Gwamna Badaru ya gyara wannan sashe inda ya yi kokarin gaske wurin ganin cewa ya tsarkake sashen ta hanyar bankado ma’aikatan bogi 4,888 da ake biya albashi, wanda wannan ya taimakawa gwamnati ta ke samun rarar N90,194,000 a kowane wata.
A lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau mulki, ya zo da alkawura guda uku da suka hada da yaki da rashawa da cin hanci, samar da tsaro da kuma fadada hanyoyin tattalin arziki.
Bangaren bunkasa tattalin arziki da Buhari ya fi bai wa muhimmanci shine noma, tsarin da shima Badaru ya bai wa muhimmanci kenan.
Tun da fari ma, Badaru a tsarin gwamnatin sa, ya yi amfani ne da samar da sauyi da ci gaba wurin zakulo irin kwarewar da jihar ke da ita a fannin noma. Wannan sai ya kasance abin da ya rika bunkasa karfin cinikayya a jihar.
Wannan tsari na sa ya yi daidai da irin wadda gwamnatin tarayya ke kokarin aiwatar wa dan ganin an rage dogaro da man fetur a kasar.
Ta hanyar anfani da cewar “Noma Sana’a ce”, a kan hakane Mai girma Gwamna ya zaburar da jama’ar jihar, musamman matasa zuwa ga sana’ar noma, wato, na duke tsohon ciniki, wanda a wannan lokacin yana tattare da matsaloli da dama da ba su dace da ci gaban zamani ba.
Wannan rashin ci gaban ya samar da koma-baya da karancin abin da ake girba, wanda ya bar manoman a cikin tsananin talauci, duk da cewa jihar tana da damammaki da suka hada da filin noma hekta miliyan 1.8 da kuma hekta 400,000 na noman fadama da za a iya anfani da shi a rani da damuna, sannan kuma ga wadatattun madatsun ruwa da za a iya samawa matasa aikin yi.
Gwamnatin Badaru ya fara da fitar da ingantaccen tsarin noma da zai sauya tsohon tsarin zuwa na zamani ta yadda zai bunkasa tattalin arzikin jihar ta hanyar samun yawaitar kayayyakin noma da kuma girbi. Gwamnatin ta command wannan nasara ne ta hanyar tsare-tsare na ci gaban noma na DFID da suka hada da SPARC, PERL, ENABLE2 da kuma GEMS3 da ke gudana a jihar.
Lokacin da ya karbi mulki a 2015, Badaru ya lura da cewa sashen ilimi na daf da rushewa. Sashen na tattare da matsaloli da suka hada da rashin gine-gine, karancin diban dalibai, rashin kwararrun malamai, rashin kayan aiki, da kuma rashin damammakin karo ilmi ga y’an jihar. Sauran matsalolin sun hada da rashin ingantattun gidajen malamai, yawaitar yara da ba sa zuwa makaranta, yawan yara da basa karatu, rashin litattafai, da kuma rashin ingantaccen tsarin ilimi da kulawa da kuma kudaden gudanarwa.
Ganin wadannan tarin matsaloli, gwamantin ta Badaru ba ta yi kasa a gwiwa ba inda ta jawo masu ruwa da tsaki a fadin jihar domin ganin an warware matsalolin. Wannan ne ya kai ga samar da wani sabon tsari mai taken canjin manufa ga tsarin ilimi a jihar, wato (Education Change Agenda) Wanda wannan ya dora sashen a kan sauyi da ka dora shi kan wani gwadabe na daki-daki wanda kuma sai dauki lokaci mai tsawo kafin a cimma nasara.
“A ziyarar da na kai wa wasu makarantu a jihar, na ga dalibai na karatu a cikin mumunar yanayi. Ba za mu amince da wannan lamarin ba. Na dauki alkawarin samar da kyakyawan yanayin karatu ga yaranmu” in ji Badaru a watan Augusta na shekara 2015.
A karkashin wannan tsarin na sauya wa sashen ilimi manufa an gina ajujuwa 6,679 tare da gyara wasu. An kuma dauki kwararrun malaman makaranta 5,973 aiki. An samar da kujerun makaranta guda 185,086 da ma gadajen kwanciya masu sama da kasa na daliban dake makarantun kwana.
Haka kuma Gwaman ya tallafa wa makarantun Islamiyya guda 516 da ke kananan hukumomi 27 dake jihar. Ya kuma samar da gidajen kwanan malamai guda 254, ofisoshi 6, dakunan kwanan daliban kananan sakandare 8, makewayu 4,746 a makarantun da ke jihar.
Duba da irin wannan gagarumin aiki, Badaru ya kafa babban tarihi da zai yi wuya a samu wanda zai wuce shi a jihar.
Ba bukatar sai an yi ta yada cewa Badaru ya yi ayyuka, wadanda ya gada da wadanda ya samar domin kuwa ya sauya akalar jihar inda ya mayar da ita jiha babba mai tsayuwa a cikin tsaraku kamar yadda aka ambata a cikin wannan rubutu. An kashe biliyoyin naira wurin ganin an inganta rayuwar al’umman jahar ta hanyar gine-gine na tituna, gadoji, samar da ruwan sha da sauran su.
Haka kuma, wani muhimmin sashe da Badaru ya inganta shine gina rayuwar matasa. Ba wanda zai karyata irin kaunar da matasa a jihar ke nuna masa saboda yadda ya inganta musu rayuwa tun daga hawan sa mulki a shekara ta 2015.
Kididdiga ta nuna cewa matasa 152,593 ne suka amfana daga dubban tsare-tsare na tallafi a karkashin gwamnatin Badaru daga 2015 zuwa 2020.
Haka kuma bincike ya nuna cewa ta hanyar anfani da tsarin koyar da sana’a, Badaru ya magance zaman banza a tsakankanin matasa a jihar Jigawa wadda ta kasance a ciki jihohi na gaba-gaba wurin da ake samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Nijeriya.
Sarari da kuma lokaci ba za su isa a iya ƙididdige irin ayyukan da Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ya aiwatar ba a cikin shekaru shida na kasancewar sa gwamnan jiha.
Duk da haka, kamar yadda masu magana ke cewa, “Ayyukan ake gani ba surutun ba” gwamna Badaru ya kawo sauyi na ci gaba a Jihar Jigawa da yayi daidai da ƙarni na 21, ta yadda a ke lissafa jihar a matsayin daya daga cikin kananan jihohin da suka samu ci gaba a ƙasar.
Wadannan nasarori da aka samu ya nuna cewa shugabanci nagari shi ne mafita wajen samar da ayyukan alheri ga jama’a. Allah Ya kara ba wa jihar mu shugabanni nagari.
Jaafaru M. Kaugama, Daga Dutse, Jihar Jigawa