Karamin Ministan Ayyuka da Gidaje Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa Buhari ya yi alwashin biyan duk wata jiha kuɗaɗen da ta kashe wajen aikin gyaran titin gwamnatin tarayya.
Ya ce ko gyara ko sake titin in dai na Gwamnatin Tarayya ne, to Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙudiri aniyar biyan jihohi kuɗaɗen da su ka kashe a wajen ayyukan.
Minista Aliyu ya yi wannan jawabi a lokacin da ya kai ziyara ga Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, a fadar sa da ke Birnin Kebbi.
Ministan ya ce ya je Jihar Kebbi domin ya tantance irin ayyukan da jihar ta yi a kan titin gwamnatin tarayya.
“Mun karaɗe tare binciko cewa daga tsaron kilomita 34,000 na titinan Gwamnantin Tarayya, muna aiki a kan kilomita 13,000 a lokaci ɗaya. Kuma an bayar da kwangilolin ga kamfanoni sama da 800 da a yanzu haka su ke kan aikin.
“Gwamnatin Tarayya za ta ba su iznin gina titina, kuma idan su ka kammala gyaran, duk za ta biya su.
“Tun kafin 2016 Gwamnantin Tarayya ta kafa kwamiti a ƙarƙashin Ministan Ayyuka, Babatunde Fashola, wanda ya gano cewa akwai jihohi 25 da su ka gina titinan gwamnatin tarayya.”
Ya tunatar da cewa ba zai manta ba a baya Shugaba Buhari ya taɓa amincewa aka biya naira biliyan 477 ga jihohi 25 da aka gamsu sun yi aikin wanda Gwamnantin Tarayya ce ya kamata ta yi masu. To wannan ne kashi na uku, wanda jihar Kebbi na cikin su, tare da jihohin Yobe da Taraba.
“Gobe kamar yanzu Minista Fashola ya na jihar Yobe domin ya duba irin wannan aiki. Yayin da Ministan Ilmi kuma zai garzaya Taraba domin duba irin wannan aiki.