Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro su tabbata sun kamo duk waɗanda ke da hannu a kasar matafiya da matsasa ɗauke da makamai suka yi Jos, Jihar Filato.
Kakakin fadar shugaban kasa, Garba shehu ya fitar da wannan sanarwa da ya ke kunshe da sakon shugaban kasa.
Sanarwar ta cigaba da cewa shugaba Buhari ya ce gwamnati ba za ta sa ka ido kawai wasu gungun bɓata gari su riki yin abinda suka dama kuma a kyale su ba.
” Wannan hari ba rikin Makiyaya da Manoma bane, wasu ne kawai suka bushi iska suka aikata hakan.
Shehu ya ce an gano cewa karara maharan sai da shirya tsaf kafin suka aikata abinda suka yi. Suka kashe wadanda zasu kashe sannan sukka jibwa wasu rauni.
Buhari ya yaba wa ƙokarin da gwamnatocin jihohin Ondo, Bauchi, Filato, Sheikh Ɗahiru Bauchi da sarkin musulmi suke yi domin tausa mutane kada abin ya fi haka
Jami’an tsaro a jihar Filato sun bayyana cewa sun kama matasa 6 cikin gungun matasan da suka tare motocin wasu matafiya da suka fito jihar Bauchi taron zikiri.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda wasu matasa ɗauke da makamai suka afka wa motocin matafiya da suka fito taron Zikiri a garin Bauchi ranar Asabar suka kashe mutane har sama da 20.
Waɗannan mutane da aka kadhe suna hanyar su ta komawa jihar Ondo ne bayan halartar taron zikiri wanda sheikh Dahiru Bauchi yayi gayyata akai.
Matasan ɗauke da muggan makamai sun tare wasu manyan motocin bas mai cin mutum 18 a hanyar Jos zuwa Zaria inda suka far musu suka kashe akalla mutum sama da 20.
Matafiyan na dawowa daga taron zikirin murnar shiga sabuwar shekarar musulunci wanda aka yi a garin Bauchi bisa gayyatar Sheikh Dahiru Bauchi.
Majiya ta bayyana cewa koda motocin suka isa gada-biyu dake karamar hukumar Jos ta Arewa sai matasan suka dira musu, suka fara sara suna duka.
” Mutum sama da 80 sun arce cikin daji. Sannan kuma na ga wasu gawarwaki har 22 waɗanda na ƙirga da kai na a asibitin koyarwa na jami’ar Jos.
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya umarci rundunar ƴan sandan jihar su bi sako-sako duk inda za shiga su tabbata sun kama waɗanan matasa da su aikata wannan mummunar abu.
Discussion about this post