Jam’iyyar PDP ta sake tuma tsalle ta haye kan Shugaba Muhammadu, ta na caccakar sa, dangane da sabon alƙawarin da ya sake ɗauka cewa zai kawar da matsalar tsaro kafin ƙarshen mulkin sa a 2023.
A ranar Alhamis ce aka ruwaito Shugaba Buhari ya sha alwashin kawar da matsalar tsaro kafin ƙarshen mulkin sa cikin 2023.
Ya yi wannan furucin ne ta bakin Mashawarci Na Musamman kan Harkokin Tsaro, Babagana Monguno, inda ya ce Buhari ya ce “ba zai bar mulki a matsayin wanda ya kasa ba.”
Matsalar ‘yan bindiga na ci gaba da tsamari a Yankin Arewa Maso Gabas da ya haɗa da Katsina mahaifar Shugaba Buhari, Zamfara, Sokoto da Kebbi.
Ko a ranar Alhamis da dare ‘yan bindiga sun tasa ƙeyar mutum 60 a ƙauyen Rini, cikin Ƙaramar Hukumar Bakura, ta Jihar Zamfara.
Akwai ɗaruruwan jama’a ciki har da ɗalibai sama da 200 yanzu haka a hannun ‘yan bindiga.
Har yanzu ana ta ja-in-ja dangane da kuɗin fanso mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara da kawunnan sa uku da kishiyar mahaifiyar sa, waɗanda ke hannun ‘yan bindiga tsawon makonni uku.
Yayin da PDP ke mayar da raddi ga Buhari, ta bayyana cewa Buhari bai yi wani abin kirki da zai iya gamsar da mutane cewa zai iya cika alƙawurran da ya ɗauka tun kafin ma ya hau mulki ba.
A kan haka PDP ta ce Buhari ya lalata ƙasar nan, kuma haka zai sauka ya bar ta a lalace, fiye da yadda ya karɓi mulkin ƙasar cikin 2015.
Kola Ologbondiyan wanda shi ne Kakakin Yaɗa Labarai na PDP, ya ce ƙoƙarin da Buhari ke yi na gyaran matsalolin Najeriya, ci gaban mai haƙar rijiya kawai ya ke yi. Kuma APC tuni ta lalace, ta ɓalɓalce, ta zama ba abin dogaro wajen ceto Najeriya ba.
Kola ya ce Shugaba Buhari da APC sun kasa wajen alƙawarin su uku na yaƙi da rashawa, samar da tsaro da kuma inganta tattalin arzikin ƙasa.
“Wane bugun ƙirji Buhari da Gwamnatin APC za su yi a lokacin da ‘yan bindiga ke kwashe mutanen da hana su kwana gidajen su har wasu na gudun hijira!
“Ina tsaro idan aka dubi yadda ‘yan ta’adda ke karkashe jama’a a ƙasar nan?”
PDP ta yi wa Buhari gori cewa hatta jihar sa ta haihuwa ba ta taɓa shiga cikin tashin hankali ba, kamar a zamanin mulkin sa.
Discussion about this post