BIKIN YUSUF BUHARI: Budaddiyar wasika ga mai dakin shugaban kasa Aisha Buhari, Daga Muhammad Bashir

0

Mai alfarma, Hajiya A’ishatu Muhammadu Buhari, mai dakin shugaban kasar Najeriya, uwar marayu. Ina fatan wannan wasika ta same ka cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali – yaya taron biki? Allah Ya albarkaci auren dan’uwan mu, Yusuf Buhari.

Mama, ni sunan na Muhammad Bashir, ni dan Najeriya ne, kuma dan asalin jihar Kano – kuma ni jikan Fulani ne asali, sabida haka ni dan’uwa ne; kuma daya daga cikin yayan ki masu kaunar ki.

Sana’a ta, ranki ya dade itace aikin jarida, ba kowa bane ni; bamu da wani mukami, ko gata sai a wurin Allah. Baba na, marigayi Malam Bashir Muhammad Idris, tsohon ma’aikacin Kamfanin Sadarwa ne na Najeriya, NITEL, kafin rasuwar sa. Sa’annan, mahaifin sa, Malam Idris Kura (Malam Idi Kura) tsohon Malamin makaranta ne, kuma ya koyar da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Dr. Rabi’u Musa kwankwaso a garin Madobi, lokacin da aiki ya kai shi can tun kafin a haife ni.

Ranki ya dade, wannan wasika ko kadan ban yi tunanin rubuta maki ita domin tozarta ki; ko raina ki; ko bata maki suna; ko Baba Buhari shugaban mu; ko aibata bikin Yusuf ba. A’a, sai domin a matsayin ki na mai dakin shugaban mu, nake ganin kamar ba bu laifi idan na rubuta maki…

Allah Ya taimake ki, ban sani ba ko kin ankara da labaran da ake yada wa a kafafen sada muzunci na zamani ba, dangane da batun rabon wayoyin hannu na alfarma da ake cewa anyi a wurin bikin Yusuf, Hajjaju Mama Shattu idan har labarin da ake yada wa na zargin cewa anyi amfani ne da kudin al’uma wajen sayen wayoyin hannu na alfarma, tare da raba wa mahalarta taron bikin cin abinci na dan shugaban kasa, Yusuf Buhari gaskiya ne, to basu kyauta ba!

Kuma wallahi, sai kun biya a Lakhera. Eh, Lakhera! Ai talakan Najeriya ba shi da wani wurin da za’a iya karbar masa hakkin sa daga hannun shugaban sa, idan ba a can Lakhera ba. Ayi hakuri idan furucin nan yayi kaushik; kuma a daure a cigaba da karanta wa. Watakila akwai abun amfani a gaba.

Amma dai magana ta gaskiya, kusan ni ba bu laifin wanda nake gani a harkar nan (idan har gaskiya ne), fiye da Mama Aisha Muhammadu Buhari – sabida shi Baba dama can wadansu mutanen sun daina daukar sa a matsayin mai gaskiya (abin takaici), A’ishatun har an fi yarda da ita, sabida karfin halin ta wajen tsage gaskiya akan kowa, har ma an ce ta taba yin yaji sabida wai “bata gamsu da irin kamun ludayin Shugaba Muhammadu Buhari a sha’anin mulki ba.”

Haba Mama A’ishatun mu, mai kungiyar Future Assured! A haka kike so mu yarda cewa akwai tabbacin samu kyakkyawar rayuwa a nan gaba? Ai ji nake, za ki nuna farin cikin ki ne dangane da wannan bikin namu, ta hanyar bayar tallafi iri-iri ga masu karamin karfi na sassan Najeriya, duk da cewa mun sani kina yin dai-dai kokarin ki – amma dai da hakan aka yi, kamar zai fi.

Amma, da girman kujerar ki ace an rarraba wa hamshakan masu kudi waya…haba, mama! Ko ni kika tambaya zan kai ki kauyukan da ba su da ruwan sha mai kyau – wanda ko iya shi aka je; aka gina masu, wallahi albarkar da Allah zai yiwa auren danki, kani na kuma dan’uwa Yusufa, ba zai misaltu ba. Mufullo sabida haka, ba kalen dangi nake ba.

Ranki ya dade, har yanzu ban yi yanke da cewa kudin al’uma din ne ku kayi amfani dasu wajen rarraba wadannan wayoyin ba, sabida Alhamdulillah mun sani dai-dai gwargwado kina da dukiya, amma dai ko da naki kudin, ko na wadansu, ko gudumawa ne aka yi amfani dasu, anyi kuskure. Koda yake, har yanzu kina da damar tuba. Ba wai bin wadanda aka baiwa za ayi a kwace ba, amma a kiyaye gaba; kuma idan da hali, a fito ayi mana jawabin yadda aka haihu a ragaya.

Talakan Najeriya fa, ranki ya dade, ko da wadansu daga cikin ku shugabanni kuna ganin kamar Allah ba ya karbar addu’ar sa, watakila sabida shi ma (wadansu) ba mutumin kirki bane, wallahi irin wannan lamarin Allah ba zai bari ba.

Idan yin jawabi ana ganin zai iya janyo matsala ko kace-nace da hayaniya, to ba bu laifi a barshi, amma kiyi magana da duk wanda yayi wannan aiki, irin maganar nan taki ta fadin gaskiya wajen ganin anyi gyara a harkar nan. Sabida ba lallai, watakila, akwai hannun ki a ciki ba. Ai ke mutuniyar kwarai ce.

Ina so kuma, wadanda suke goya maku baya (a makance, wadanda ke ma mun sani ba burge ki suke ba), su daina tumasanci; suna take gaskiya al-hali suna sane. Su sani cewa wannan ba dai-dai bane – kuma lallai sai sun yi bayani a Ranar Al-Qiyamah.

A karshe, ina kara taya ki murna da aka kammala wannan bikin lafiya, domin mu da muke nesa da ku har yanzu bamu ji wani bakin labari ba, dangane da wannan bikin, kuma Allah Ya sani, iyaka wannan ma ya ishe mu farin ciki. Allah Ya sanya masu alkhairi da albarka. Alhamdulillah!

Allah Ya ba da ikon yin gyara, Ya taimaki shugabannin mu na fadin Najeriya; Ya kara mana kwanciyar hankali da zama lafiya da wadata.

Muhammad Bashir, mazaunin garin Kano ne a Arewacin Najeriya.
Za’a iya samun sa a lambar waya +2348062958059, +2348099657585 ko kuma email a muhammadbashir38@gmail.com

Share.

game da Author