Wata ƙungiya mai kiran kan ta Arewa Youth Advisory Forum (AYCF), ta jawo hankalin Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta hana shirin BBNaija kwata-kwata.
Shugaban AYCF Yerima Shettima ya bayyana shirin da cewa ‘bala’i ne a cikin al’umma’, kamar yadda Daily Trust ta yi hira da shi a ranar Juma’a.
Shettima ya ce bai kamata gwamnatin tarayya ta bari ana nuna shirin a tashoshin talbijin ba, saboda ana nuna haɗala, tsiraici da iskanci a ciki.
“Ni a gare ni shirin wani bala’i ne. Ban yi amanna da shirin BBNaija ba, saboda shirin ya na nuna iskanci da fasiƙanci ƙarara. Irin wannan haɗala bai kamata a ce gwamnati ce ke ƙarfafa yin ta ko nuna ta ga al’umma ba.
“Na sha bayyana cewa wannan shiri dai shirin tallata fasiƙanci da baɗala ne a zukatan matasa da ƙananan yara, don haka a soke nunawa da shirin shirin kwata-kwata.
“Za ka ga mutane da yawa sun ƙura ido su na kallon ana tafka fasiƙanci, mata na nuna tubarruji da tsiraicin su a fili, sun maida shirin kamar fina-finan batsa. Bai kamata ana ɗaure wa fasiƙai gindi su na irin wannan baɗalar ba.
“Ina kiran duk masu ƙaunar ƙasar nan da alkhairi su haɗu su bai wa gwamnati shawara, su jawo hankalin ta wajen nuna mata illar wannan iskanci da ake nunawa a talabijin domin a daina shirin kwata-kwata.”
Shirin BBNaija Tallata Fasiƙanci Ne -Limamin Cocin Angalika Na Abuja:
Idan ba a manta ba, ba wannan ne karo na farko da aka soki shirin BBNaija ba.
Limamin Cocin Angalika na Abuja, Ifeanyi Akunna, ya taɓa yin kira da daina nuna shirin baki ɗaya, kuma ya ce shirin fasiƙanci ne kawai ake koya wa matasa.
Limamin ya ce wata hanya ce kawai aka ƙirƙiro wadda Shaiɗan zai samu damar mamaye zukatan matasan ƙasar nan, ta yadda nan gaba za a dattawan ƙwarai a cikin al’ummar mu.
Discussion about this post