BBABBAR KAMU: Sanata Stella da ake zargi da handame sama da naira biliyan 2 ta tsunduma APC

0

Tsohuwar ministar sufurin jiragen sama da hukumar EFCC ke zargin ta da handame biliyoyin nairori ta tsunduma APC ranar Alhamis.

Stella Oduah na daga cikin ƴan gaban goshin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a lokacin da ya ke mulki.

Sai dai tun kafin ta sauka daga kujerar mulki EFCC ta fara tuhumarta da zargin handame wasu biliyoyin nairori a ma’aikatar sufurin jiragen sama.

A ranar Alhamis shugaban jam’iyyar APC nab rikon kwarya kuma gwamnan jihar Yobe, Mala Buni da wasu gwamnoni da jigajigannAPC sun amshi Oduah da hannun bibiyu.

An wanke ta tas a hedikwatar jam’iyyar a APC dake Abuja sannan aka yi mata yar gaeruwa kwarya-kwaryar biki da daukan hotuna.

A jawabin da ta yi Oduah ta ce ta tsallako zuwa APC daga PDP ne domin ta haɗa hannu da gwamnati mai ci domin kawo ci gaba a yankin kudu maso Gabashin Najeriya.

Cikin wadanda suka wanke Oduah akwai gwamnoni jihohin Kebbi, da Imo sannan akwai mataimakin shugaban majalisar Dattawa sanata OmoAgege.

Share.

game da Author