Akalla ɗalibai 132 mahara suka sako ranar Alhamis da dare bayan shafe kwanaki 86 tsare a hannun su.
Kasimu Barangana wanda shi ne ya yi dakon ƙudin fansar ɗaliban a wancan lokacin ya tabbatar wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa an sako ɗaliban a karamar Hukumar Birnin Gwari ne dake jihar Kaduna.
Haka shima Ɗanladi Idon-Duniya, shugaban kungiyar direbobi na Kasa, ya tabbatar da sakin ɗaliban yana mai cewa yana daga cikin waɗanda mahara suka mika wa ɗaliban.
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=m7uMI1fRK_k&w=760&h=388]