BAYAN KISAN MANOMA DA TATSE MASU KUƊAƊEN FANSA: Gwamnatin Tarayya ta bai wa Katsina naira biliyan 6.2 don inganta rayuwar Fulani makiyaya

0

Yayin da Fulanin cikin dazuka ke ci gaba da yi wa manoma ragargazar kisa, garkuwa da tatsar maƙudan miliyoyin kuɗaɗen fansa a hannun manoman, Gwamnantin Tarayya ta yi biris da zancen diyyar rayukan da Fulani ke kashewa da kwashe wa dukiya a Katsina, ta kamfaci naira biliyan 6.2 ta bai wa jihar domin a inganta rayuwar Fulani makiyaya.

Gwamna Aminu Masari na Jihar Katsina ne ya bayyana cewa Gwamnatin Katsina ta karɓi kuɗin har naira biliyan 6 25, daga Gwamnatin Tarayya domin gina wa Fulani rugagen kiwo na zamani a killace.

Wannan gagarimin aiki inji gwamnan zai kawo ƙarshen rigingimun da ake yi tsakanin manoma da makiyaya, wanda ya yi sanadiyar haifar da Fulani ‘yan bindiga a jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Masari ya tabbatar da karɓar kuɗaɗen a lokacin da ya ke bayani a wani taron makomar matsalar tsaro a Afrika, a Cibiyar Nazarin Matsalar Tsaro a ranar Litinin, a Abuja.

“Ina tabbatar maku Jihar Katsina har ya karɓi naira biliyan 6.25 waɗanda Gwamnantin Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alƙawarin bayarwa, domin gina wuraren kiwo da matsugunan Fulani makiyaya a dazukan Katsina”

Masari ya ce aiki zai ƙunshi gina hanyoyin burji na cikin dazuka, mayankar dabbobi, rijiyoyin burtsatse masu aiki da hasken rana, ofishin ‘yan sanda da rugagen wuraren kiwon shanu.

Ya ce kuma aikin zai haɗa da farfaɗo da kayayyakin inganta rayuwar mutanen karkara da su ka haɗa da madatsun ruwa, makarantu, asibitocin sha-ka-tafi, asibitocin duba lafiyar dabbobi da kuma kula da dazukan kiwon dabbobi.

Ya ce kashin farko na aikin zai ƙunshi faɗin ƙasa 7000 ta kiwon shanu, daga cikin kadada 122,000 da ke cikin Dajin Rugu.

“Ƙananan Hukumomi 10 da ke fama da ‘yan bindiga ne za a fara aiwatar da aikin a cikin su.

Sun haɗa da Jibiya, Batsari, Kurfi, Dutsinma, Safana, Ɗanmusa, Ƙanƙara, Faskari, Sabuwa da Ɗandume.” Inji Masari.

Share.

game da Author