Wasu ‘yan ta’addar da aka tabbatar cewa ‘yan ISWAP ne, sun fasa garin Rann da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kala Balge a Jihar Barno.
An tabbatar da cewa sun kai wa wani sansanin sojoji hari da kuma wasu wurare, kamar yadda PR Nigeria ta tabbatar.
Rahoton ya ce maharan su na da yawan gaske, kuma sun kutsa cikin garin bayan sun riƙa yin harbe-harbe a sama, sun firgita jama’a.
Rahoton ya ce an ga mutanen garin sun tsere a cikin daji, su kuma jami’an bayar da agaji aka ce an ga su na nausawa kan iyakar Najeriya da ƙasar Kamaru.
ISWAP sun kai harin a Rann a lokacin da ake samun yawaitar ‘yan Boko Haram masu miƙa wuya.
Kwanan nan Gwamnantin Jihar Barno ta ce akwai aƙalla ‘yan Boko Haram 3,000 da su ka yi saranda ga Sojojin Najeriya.
Gwamna Babagana Zulum ya ce baya ga waɗannan 3,000 ɗin, akwai kuma wasu 900 da su ka yi saranda ga Sojojin Kamaru.
Ba wannan ne karo na farko ko na biyu da ‘yan ta’adda su ka kai farmaki a garin Rann ba.
An kai wa garin hari sau uku a cikin shekaru uku da su ka gabata, inda aka kashe ɗari ruwan jama’a, wasu ɗaruruwan kuma su ka gudu su ka bar gidajen su.
A Rann ne kuma Sojojin Saman Najeriya su ka jefa bam a cikin sansanin masu gudun hijira a bisa kuskure, cikin 2017, har sama da mutum 200 su ka mutu.