BARKEWAR KWALARA A AREWA: Kwalara ta kashe mutum 146 cikin mako ɗaya a jihar Kebbi

0

Akalla mutum 146 ne suka rasu a dalilin kamuwa da cutar Amai da Gudawa Kwalara a jihar Kebbi.

Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda cutar ke yaduwa a jihohin yankin Arewa maso Yammacin kasar nan.

Bisa ga rahoton mutum 75 sun mutu a jihar Katsina, Zamfara mutum 30, Sokoto 23 da Kano 119.

Da yake tattaunawa da wakilin gidan jaridar ranar Laraba shugaban asibitin ‘Yahaya Memorial’ Aminu Bunza Wanda ya tabbatar da barkewar cutar a jihar inda ya kara da cewa cutar ta fara barkewa a kauyen Dirin daji ne dake karamar hukumar Sakaba.

Bunza ya ce zuwa yanzu mutum 2,028 sun kamu kwalara a jihar kuma cutar ta yadu zuwa kananan hukumomin 20 na jihar.

Ya ce gwamnati ta wadatar da asibitocin dake kananan hukumomi jihar da kayan gwajin cutar da magunguna sannan ta horas da jami’an lafiya kan yadda za su rika kula da marasa lafiya domin dakile yaduwar cutar.

Bunza ya yi kira ga mutane da su rika tsaftace jikin su, muhalli da abincin su domin gujewa kamuwa da cutar.

“Da an ji ba dai-dai ba a ji a gaggauta zuwa asibiti domin samun magani.

Ya yi kira ga jami’an lafiya da kada su rika bai wa marasa lafiya magani a gida amma su rika garfafa gwiwowin mutane wajen zuwa asibiti da zaran sun fara rashin lafiya.

Share.

game da Author