BAKARE YA ZUNGURI GOSHIN OYEDEPO: ‘Sai ka yi ta yi wa mutane kuri da alfahari da jirgi kamar a kan ka farau’

0

Shugaban cocin Citadel Global Community Church (tsohon cocin Latter Rain Assembly), Tunde Bakare, ya bayyana cewa baya gaba da fasto David Oyedepo duk da ko ra’ayoyin su bai zo ɗaya ba.

Oyedepo shine shugaban cocin ‘Winners Chapel’.

Bakare ya faɗi hakan ne a wani Shirin talbijin din TVC da aka yi ranar Asabar.

Bakare wanda tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a 2011, ya kara bada haske kan abokantakan sa da fastocin wannan zamani.

” Ni da Oyedepo a shekara ɗaya aka haife mu, sa’o’i muke. An haifi Oyedepo a Agusta, 1954 ni kuma a Satumbar 1954.

“Ra’ayoyin mu da ababen da muka yi Imani da su ya banbanta sai dai hakan ba shine zai sa mu zama abokan gaba ba.

Ya ce wata rana ya shiga jirgin tare da Oyedepo inda wani da ya hango shi ya zo ya gaishe shi.
Bakare ya ce mutum ya ƙasa gaishe shi saboda ya ga yana zaune kusa da Oyedepo.

“Banbancin dake tsakanin na da Oyedepo bai shafi yada bisharar da muke yi ba sannan bana gaba da wani faston dake yake yin wa’azi don Allah

Ya ce shi bai ga dalilin da ya sa Oyedepo yake yin kuri da jirgin saman da yake da shi ba
“Kafin Oyedepo ya siya jirginsa Ina da jirgin sama kirar 1707 dake dauke da tambarin coci na amma babu wanda ya sani saboda ban taɓa ce wa kowa jirgin wa ba ne.

“Muna amfani da jirgin domin kasuwanci saboda gwamma na kashe kudi kadan na je duk inda zani da na siya jirgi ina shiga domin jawo hankalin mutane.

Bakare ya ce kafin na bude coci na na yi aure a cocin ‘Redeemed Christian Church of God’ sannan shugaban cocin shine ya tsaya a matsayin mahaifina, Enoch Adeboye.

“Na kuma yi aiki da cocin Deeper Life na tsawon shekara biyar sannan har yanzu Ina zumunci tare da Adeboye da William Kumuyi a matsayin mahaifana.

Arangamar Bakare da Oyedepo

Bakare ya ce zai mara wa duk faston dake yin bishara ta hanyar gaskiya amma a duk lokacin da ya ga wani fasto yana bishara ta hanyar karya domin kawai ya samu mutane zai kwabe shi.

“Abokin gaskiya shine Wanda zai iya nuna maka laifin ka ba wanda zai rika cutar ka yana boye maka ba.

Bakare ya ce Oyedepo ya tabbatar masa cewa ya rubuta karya wata takarda da ya rubuta.

Ya kuma yi magana kan siyasa, rashawa da cin hancin da ake fama da shi a kasar nan.

Share.

game da Author