Ba zan ci gaba da zama dan Najeriya ba idan har Tinubu ya zama shugaban Kasa – Bode George

0

Jigo a jam’iyyar PDP wanda ya rike mukamin mataimakin shugaban Jam’iyyar na yankin Kudu, ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da zama dan Najeriya ba idan Tinubu ya zama shugaban kasa a 2023.

Tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu kuma jigo a jam’iyyar APC ke kan gaba wajen zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC idan wa’adin buhari ya cika a 2023.

Sai dai kuma wa hira da Bode George yayi da Talbijin din Aris, ranar Laraba ya ce ba zai iya ci gaba da zama dan Najeriya ba idan har Tinubu ya zama shugaban kasa a 2023.

” Kowa ya sanko Tinubu waye, ya tattara jihar Legas ya saka shi a cikin aljihun sai yadda yai da kudaden shiga na jihar. Yaya za ace wai mutum daya na samun naira biliyan 9 daga aljihun gwamnati haka kawai. Gaba daya shine wuka shine nama. Yana da mahaukatan kudin da ja da shi ma ba zai yiwu ba saboda karfin arziki da ya ke dashi

” Naji wani tsohon minista a PDP wanda ya koma APC yanzu kuma dan gaban goshin Tinubu, Ogunlewe yana ikirarin cewa Tinubu ne ya fi dacewa ya shugabanci kasar nan a 2023. Ina tabbatar muku da cewa wannan minista ya zauce domin shine a baya yake surfa ma Tinubu zagi da tallata gazawar tinubu a lokacin da yake gwamna a jihar Legas. Amma yanzu wai shine ke yabon sa saboda ba shi da kunya.

George ya ce idan Ogunlewe ya isa su hadu ko da a makabarta ne su yi mukabala cikin dare sai yayi ragaraga da shi.

Bayan haka ya zargi tinubu da rashin yin makaranta inda ya kalubalance shi da ya fito ya nuna takardun Kammala makarantun sa tun daga Firamare.

” Mun kalubalance shi tun yana gwamnan Legas amma ya kasa fiddo su sai kame kame ya ke yi.

Daga nan kuma ya zargi Tinubu da dasa sojojin haya a jam’iyyar PDP suna kawo masa sirrin jam’iyyar.

” Saboda karfin arzikin Tinubu, har sojojin haya ya daddasa a cikin jam’iyyar PDP tun daga uwar jam’iyyar zuwa jihohi. Suna yamutsa al’amurorin jam’iyyar sannan suna kawo masa bayanan duk abinda ke faruwa jam’iyyar. Shi yake ya mutsamana jam’iyya ta bayan fage ba a sani ba. Mutanen Tinubu ne birjik a PDP, sun dagula jam’iyyar suna kuma kai masa rahoto akan jam’iyyar.

” Wai kuma ace irin wannan mutum ne zai zama shugaba a kasar nan sannan a yarda da haka.

Share.

game da Author