Ba za mu yarda a sake yi wa malaman Kaduna jarabawa bayan wadanda aka yiyyi a baya ba – Kungiyar Malamai

0

Kungiyar Malaman Najeriya (NUT), reshen jihar Kaduna ta ce babu wani malamin Makarantar Firamare a jihar da zai sake zama rubuta jarabawar cancanta wanda da Gwamnatin Jihar ke kokarin hiryawa yanzu haka.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan an tashi taron gaggawa da ta yi a Kaduna ranar Laraba.

A cikin wata sanarwar, wanda Shugaban kungiyar ta jiha Ibrahim Dalhatu, da Mataimakin Babban Sakataren kungiyar Adamu Ango suka saka hannu, kungiyar ta bada shawarar maimakon haka gwamnati ta yi amfani da kudaden da ta ware domin tantance malaman wajen horas da su.

Idan ba a manta ba a watan Janairun 2018, gwamnatin ta sallami malamai 22,000 saboda faduwa jarabawar cancanta da aka gudanar a shekarar 2017.

Kuma a ranar 14 ga Yuli 2021 gwamnati ta sanar da shirin sake gudanar da jarabawar cancanta ga malaman firamare domin tabbatar da ingantaccen koyarwar da suke yi a makarantun firamaren jihar.

Kungiyar ta ce rubuta jarrabawar cancantar ba shine ke nuna kwarewar malami a aikinsa ba.

“Ana iya tantance ƙwarewar malami a cikin aji sannan gwajin ƙarshe da aka yi ya taimaka wajen samar da kwararrun malaman dake koyarwa a makarantun bokon jihar.

NUT ta ce bata amince da yadda gwamnati ke tattance kwarewar malamai ba domin tattance kwarewar malamai ba na gwamnati bane kadai ba.

Kungiyar ta ce za ta amince da tattance malamai idan gwamnati ta hada gwiwa da hukumomin da ya kamata kamar Majalisar Rijistar Malamai.

Share.

game da Author