Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya yi watsi da surutan bayan fage da ake yi cewa shi ne ya ruruta wutar rikicin jam’iyyar PDP wanda ke neman zama gobarar jam’iyya a yanzu.
Atiku na ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP da ake nunawa da yatsa cewa su na ƙoƙarin tumɓuke Shugaban PDP na Ƙasa, Uche Secondus.
Atiku ya bayyana cewa shi ƙoƙarin tabbatar da haɗin kai da kuma ɗinke ɓaraka ya yi a cikin PDP, maimakon ruruta wutar rikicin da wasu ke cewa ya yi.
Ya ce ya goyi bayan sasantawa da kuma haɗin kan jam’iyyar PDP kamar yadda aka ga ya riƙa yi a baya-bayan nan.
Daga nan ya yi kira da kowa ya haƙura, a maidai takubba cikin kube, domin ci gaban PDP a ƙasa baki ɗaya.
Atiku ya ce bai kamata jam’iyyar adawa ta faɗa cikin rikici ba, a daidai lokacin da jam’iyya mai mulki ta kasa cika wa al’umma alƙawurra, kuma a lokacin da ‘yan Najeriya su ka gaji da mulkin ta.
Ya ce ya kamata a samu haɗin kai a PDP, domin a kawar da APC a zaɓen 2023.
“Duk masu son ci gaba da mulki ko da talakawan ƙasar nan ba su so ne ke ta ruruta wutar rikice-rikice a cikin PDP, don kada mulki ya suɓuce daga hannun sa idan zaɓen 2023 ya zo.”