Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta kama wani mutum mai shekaru 33 da laifin yi wa ƴar shekara 27 fyaɗe a jihar.
Kakakin rundunar DSP Abimbola Oyeyemi ya ce rundunar ta kama mutumin ne ranar Asabar bayan matar da ya yi wa fyaden ta kai kara a ofishin ‘yan sanda dake Sakora, Sagamu.
Matar ta bayyana wa jami’an tsaron cewa mutumin ya danne ta ne wai don a cewar sa bata gai she shi idan ta ganshi, shine ya yi mata hukunci da yi mata fyaɗe.
“Mutumin ya lakada min dukan tsiya sannan ya ciccibeni da karfin tsiya zuwa bayan gidansa ya yayyaga min riga yayi lalata da ni.
Oyeyemi ya ce bayan haka sai ya aika da ‘yan sanda inda tare da taimakon mutane aka kamo wannan mutum.
Sai dai kuma ya shaida wa yan sanda cewa ba da gangar ya aikata abinda yayi ba, a lokacin ya narki giya iya giya, bai ma san abinda ya ke yi ba har ya danne ta da karfin tsiya yayai lalata da iat.
Ya ce matar ta je asibiti domin likitoci su dubata.
Oyeyemi ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bada umurin a kai karar zuwa fannin dake gurfanar da masu aikata laifuka irin haka na jihar. Ya ce za a maka mutumin a kotu da zarar an kammala bincike.
Discussion about this post