AREWA A HANNUN ‘YAN BINDIGA: Yadda ake tayi da neman ragin kuɗin fanso mahaifin Kakakin Majalisar Zamfara da ya shafe kwanaki 11 a hannun ‘yan bindiga

0

Kamar yadda ake cinikin gida ko gona a shafe kwana da kwanaki ana shawarwari bayan mai saye ya taya, shi kuma mai kadara ya ce ‘albarka’, to haka ake ci gaba da ciniki ko tattauna neman ragin kuɗin fanso mahaifin Kakakin Majalisar Jihar Zamfara wanda ‘yan bindiga su ka arce da shi tun a ranar 4 Ga Agusta.

Majiya mai tushe ta ce lamari ya yi tsauri sosai har sai da ta kai an nemi agajin gogarman ‘yan bindiga Halilu Kachalla, domin ya shiga tsakani da gogarman da ya jagoranci sace dattijon da nufin neman sassauci maƙudan kuɗaɗen fansa da ‘yan bindigar su ka nemi a biya su.

Tun dai washegarin da su ka sace mahaifin na Honorabul Nasiru Magarya tare da kishiyar mahaifiyar Kakakin Majalisar ta Zamfara da wasu kawunan sa biyu da sauran ‘yan uwa uku, maharan sun nemi a biya su naira miliyan 500 cur kafin a sako su sake su.

Wani babban hadimin Kakakin Majalisar da ba ya so PREMIUM TIMES ta bayyana sunan sa ne shaida wa jaridar nan cewa naira miliyan 500 ‘yan bindigar su ka nemi a biya su, kwana bayan sun sace mutanen daga Magarya, mahaifar Kakakin Majalisar Jigawa.

PREMIUM TIMES ta kuma ji cewa akwai wani tsohon kwamishinan Zamfara ɗan asalin garin Zurmi, wanda kusan shi ne ma jagoran tawagar da ke tattauna neman ragin kuɗin fansar.

Sannan kuma akwai wasu daga cikin jami’an gwamnati da kuma wasu abokai na Kakakin Majalisa.

Sai dai makusancin ya nuna cewa lamarin wata ƙullalliya ce kawai aka shirya don a tatsi kuɗaɗe a hannun kakakin.

“Sun nemi a biya su kuɗin fansa naira miliyan 500, mun ce masu ba mu da waɗannan kuɗaɗe, kuma babu inda za mu same su.

“Daga nan kuma mun riƙe su har su ka sassauto da farashi ƙasa zuwa naira miliyan 200. Mu ka ce ba mu da waɗannan kuɗaɗen.

“Daga nan fa su ka nemi mu hanzarta mu biya, saboda ba su son su taɓa lafiyar dattawa.”

PREMIUM TIMES ta ji daga majiya cewa ‘yan bindiga su nemi daddalewa a kan naira miliyan 100, saboda a cewar su, ba sansanin ‘yan bindiga ɗaya ba ne su ka je kamo iyayen na Kakakin Majalisar Zamfara.

“Sun ce daga sansanonin su daban-daban su ka yi gangamin wakilai. Don haka su na buƙatar kuɗaɗen domin sallamar kowane sansani.”

Majiyar ta ce an shaida masu sansanonin sun fi shida, don haka su na neman sai dai a biya kowane sansani naira miliyan biyar.

An Nemi Sa-hannun Gogarma Kachalla:

Majiyar PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa tun bayan yin garkuwa da mutanen, wani jami’in Ƙaramar Hukumar Shinkafi ya tunruɓi gogarma Kachalla, wanda ya ƙulla yarjejeniyar daina kai hare-hare shi da gwamnatin Zamfara. An zargi Kachalla ne saboda a yankin sa ne lamarin ya faru.

Kachalla shi ma ya tuntuɓi Turji da ke riƙe da dazukan Zurmi da wasu yankuna na Jihar Katsina.

Yayin da har yanzu ba za a iya tabbatar da a hannun waɗanda mutanen su ke ba, an dai ji cewa sansanoni daban-daban ne su ka yi gangami su ka kame su.

Har yanzu dai ana ci gaba da tattaunawa, zuwa lokacin da aka rubuta wannan labari.

Kachalla ya tabbatar masu cewa ba shi ne ya yi garkuwa da mahaifin na Kakakin Majalisa ba.

Share.

game da Author