Masu garkuwa da mutane, waɗanda aka tabbatar da cewa su na riƙe da manya-manyan makamai, sun yi gaba da Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar Neja, Mohammed Idris.
Sakataren Gwamnantin Jihar Neja, Ahmed Matane ya shaida haka a wata wayar da ya yi da NAN a ranar Litinin ɗin nan da safe.
Ya ce wasu musu garkuwa ne su 15, kowanen su ɗauke da zabga zabgan bindigogi, su ka yi gaba da Kwamishinan wajen ƙarfe 11 na dare a lokacin da ake zabga ruwan sama.
Har zuwa lokacin da ya ke bayanin dai masu garkuwar ba su tuntuɓi kowa ba tukunna, ballantana a ji halin da ya ke ciki.
Ita ma Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Abubakar Bello na Neja, Mery Noel-Berge ta tabbatar da sace kwanisihinan. Sai dai ita cewa ta yi wajen ƙarfe 1 na dare aka tafi da shi.
“Wajen ƙarfe 2 na dare aka y garkuwa da shi a gidan sa da ke Babban Tunga, cikin Ƙaramar Hukumar Tafa.”
Kakakin Yaɗa Labaran Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da labarin, kuma ya ce zaratan ‘yan sanda sun bazama bin sawun maharan domin su ƙwato shi.