‘Yan bindiga sun kai mummunan hari a ƙauyen Goran Namaye, inda su ka kashe mutum huɗu, kuma su ka arce da mutum 50.
Lamarin ya faru a Goran Namaye, garin da ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Maradun, kan iyaka da Karamar Hukumar Bakura, a lokacin jijjifin asubahin Litinin.
Rundunar ‘yan Sandan Zamfara ta tabbatar da kisan da kuma adadin waɗanda aka gudu da su.
Sai dai majiya da dama sun tabbatar da cewa waɗanda aka tafi da su sun zarce 70. Kuma mutum 10 aka kashe, ba huɗu ba.
Majiya ta ce maharan sun shafe awa biyar a cikin garin.
Hamza Bakura ya shaida wa wakilin mu cewa wajen ƙarfe 1 na dare ‘yan bindigar su ka isa ƙauyen.
“Nan take su ka fara harbi, kuma waɗanda su ka kashe, yankan rago su ka yi masu ba kisa ba ne na harbi.”
Ya ƙara da cewa sai wajen ƙarfe 4 na asubahi jami’an tsaro su ka isa, kuma maharan su ka tare su gadan-gadan suka riƙa buɗe wa juna wuta.
Wani ɗan Talata Mafara mai suna Mudassir Muhammad, ya ce “waɗanda aka arce da su za su fi mutum 70.”
“Yanzu haka akwai mutum zai kai 50 da ke gudun hijira a gidan mu nan Mafara. Kuma a ƙasa ƙasa su ka gudo, tun daga Goran Namaye.”
Tun bayan da jiragen yaƙi su ka fatattake su a Dajin Sububu, ‘yan bindiga sun maida hankali wajen kai hare-haren su a yankin Bakura, Maradun da Talata Mafara.
Ranar Alhamis sun sace mutum 60 a ƙauyen Rini, bayan sun kwashi ɗalibai a ‘Yarkuforoji cikin Ƙaramar Hukumar Bakura, kusa da Goran Mamaye.
Ana zargin yaran Halilu Kachalla ne su ka kai hare-haren.
‘Yarkuforoji can ne mahaifar shahararren ɗan dambe Shago. Goran Namaye kuma can ne mahaifar fitaccen mawaƙin da ya yi rayuwar sa a Zaria, Hassan Wayam.