Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ta hana cin dukkan kasuwannin mako-mako a faɗin jihar.
Matawalle ya bayyana hakan ne a matsayin ɗaya daga cikin matakan da gwmnai jihar ta ɗauka domin daƙile matsalar ‘yan bindiga.
Ya yi sanarwar a lokacin da ya karɓi ɗalibai 18 na Kwalejin Koyon Aikin Noma da Kiwo ta Bakura, waɗanda ‘yan bindiga su ka saki a ranar Juma’a.
Haka kuma Matawalle ya hana sayar da fetur a galan da jarkoki. Sannan ya hana gidajen mai su sayar da fetur na sama da naira 10,000 ga mota ɗaya.
Sauran dokokin da aka ƙaƙaba sun haɗa da hana lodin shanu ko kayan abinci daga wannan wuri zuwa wancan.
Haka nan an hana yawo da babur daga ƙarfe 8 na dare zuwa ƙarfe 6 na safiya a cikin garuruwa.
Amma dokar ta ce a ƙauyuka ko cikin daji, tun daga ƙarfe 6 na yamma za a daina hawa babur.
Dokar ta haramta ganin mutum uku a kan babur ɗaya.
Sai dai dokar ta yi sassaucin ganin jami’an tsaro, na kiwon lafiya, ‘yan jarida da wasu masu ayyuka na musamman wajen karakaina kan babur bayan ƙarfe 8 na dare. Amma ko su din, sai da katin shaida.
Gwamna Matawalle ya gargaɗi gidajen sayar da fetur cewa su riƙa kula kada motoci da babura su riƙa komawa sayen fetur jim kaɗan bayan sun saya.
Premium Times ta buga labarin da Gwamnan Zamfara ya nemi a kafa dokar-ta-ɓaci.
Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara, ya roƙi Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaƙaba dokar-ta-ɓaci a kan matsalar tsaro, domin a cewar sa, hakan ne kaɗai zai iya magance taɓarɓarewar da tsaro ya yi.
Da ya ke buga misali da jihar sa Zamfara a lokacin da Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Shiyyar Kebbi, Sokoto da Zamfara, AIG Ali Janga ya kai masa ziyara, Matawalle ya bayyana cewa kafa dokar-ta-ɓaci a fannin tsaro ne kaɗai zaɓin da ya rage, domin a magance matsalar.
Ya ce a kullum Zamfara na cikin hare-hare, ta yadda lamarin ya yi ƙazancewar da in ba dokar-ta-ɓaci aka kafa ba, to ba za a iya shawo kan matsalolin ba.
“Ba wanda zai iya bugun ƙirji ya ce ya tsira, ko ya tsallake matsalar tsaron nan. Saboda haka a kafa dokar-ta-ɓaci kan sha’anin tsaro kawai.”
Matawalle ya yi wa AIG Janga wannan bayani ne a cikin wata sanarwar da Jami’in Yaɗa Labarai Zailani Baffa ya fitar a Gusau, babban birnin jihar Zamfara a ranar Laraba.
AIG ya samu rakiyar Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Zamfara, a ziyarar da su ka kai wa Gwmana Matawalle.
A wani jawabi da Matawalle ya yi aka watsa a jihar, ya zargi ‘yan siyasa da yi wa shirin sa na zaman sulhu da ‘yan bindiga domin a samu zaman lafiya a jihar.
Ya ce lamarin tsaron Zamfara ya sha bambam da na sauran jihohi.
Matawalle ya kuma zargi wasu gwamnoni na Arewa maso Yamma da ƙin yin sulhu da ‘yan bindiga, lamarin da ya ce ya ƙara gurgunta duk wani ƙoƙarin da ya yi na samar da zaman lafiya a Zamfara.
AIG Janga da Kwamishinan ‘Yan Sanda Ayuba Elkhana sun jinjina wa Gwamna Matawalle, wajen ƙoƙarin da ya ke yi na bayar da goyon baya ga ‘yan sandan jihar domin samun zaman lafiya.
Discussion about this post