AREWA A HANNUN ƳAN BINDIGA: Yadda mahara suka sace mahaifin Kakakin majalisar jihar Zamfara, Kawun sa da Kishiyar Mahaifin sa

0

Ƴan bindiga sun yi takakkiya har cikin ƙauyen Magarya kuma su ka yi gaba da mahaifin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Nasir Magarya.

Sun gudu da shi da matar sa da wasu mutane huɗu.

Kakakin ‘Yan Sandan Zamfara, Mohammed Shehu ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da labarin sace dattijon a ranar Laraba da yamma, amma bai yi wani ƙarin haske ba.

Sai dai ya ƙara da cewa tuni Kwamishinan ‘Yan Sandan Zamfara Hussaini Rabiu ya tura zaratan ‘yan sanda cikin daji, domin su ceto waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin.

Majiyoyi sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa an sace mahaifin na Kakakin Majalisar Zamfara a gidan sa da ke Magarya, cikin Ƙaramar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara.

“Sun shigo da la’asar sakaliya a lokacin da ake jam’in Sallar La’asar. Su ka riƙa harbi sama, yayin da su ka tunkari gidan sa.”

Wata majiya kuma ta ce a ranar sai da ‘yan bindigar su ka kai farmaki a ƙauyukan Kaiwa, Lamba, Jinkirawa da Sabon Fegi, duk a cikin Ƙaramar Hukumar Zurmi a ranar Laraba ɗin.

Kakakin Yaɗa Labarai na Kakakin Majalisar Zamfara mai suna Mustapha Jaafar ya ce wa wakilin mu ya jira sanarwa daga jami’an gwamnati tukunna.

Majiya da kuma wasu rahotanni sun tabbatar da cewa sauran mutum biyar da aka yi gaba da su tare da mahaifin Kakakin Majalisar na Zamfara, sun haɗa har da kawun sa da kuma kishiyar mahaifiyar sa.

Ba wannan ne karon farko da su ka shiga ƙauyen ba. A baya sun shiga sun kwashe dabbobi da dukiya kuma su ka kashe mutum uku.

Share.

game da Author