AREWA A HANNUN ƳAN BINDIGA: Cikin kwanaki uku a jere, mahara sun sake kashe wasu mutane, sun yi garkuwa da mutum 17 a Zamfara

0

Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda wasu ƴan bindiga suka kashe wata mata maijego da jaririnta a ƙaramar hukumar Maru, ranar Lahadi.

A daidai ƴan bindiga suna aikata wannan mummunar kisa da suka kai a Maru, A Bakura wasu bangaren ƴan bindiga na sace ɗaliban kwalejin koyan ayyukan gona.

Wani basarake a karamar hukumar Maru ya shaida wa wakilin mu cewa maharan da yawa daga cikin waɗanda aka sace wasu daban sun gudu da ga ƴan bindigan a lokacin da suke nausawa daji da su.

Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa mahara akalla su 50 ɗauke da bindigogi tsirara da rana tsaka suka buɗe wa motar hawa da ya taso daga Jibiya zuwa Zurmi a jihar Zamfara.

” A cikin waɗanda aka kashe akwai siriki na Alhaji Muntari Ziza da ɗan sa, wanda zai je kasuwar Zurmi, shi ɗan kasuwa ne. A nan muka tsinci gawarwakin su.

Bayan haka maharan sun nausa cikin daji da wasu matafiyan.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda ƴan bindiga suka afka makarantar koyon aikin Noma dake garin Bakura, suka sace ɗalibai da wasu daga cikinsu malaman makarantar.

Rajistaran kwalejin Aliyu Bakura ya bayyana cewa maharan sun sace ɗalibai 15 da wani malami da matar sa.

” Ƴan bindigan sun shigo makarantan ɗauke manyan makamai. Sun kashe jami’an tsaro hudu har da ƴan sanda.

Har yanzu akwai ɗalibai da dama dake tsare hannun ƴan bindiga ba a sako su ba.

A jihar Neja, har yanzu ƴan makarantan Islamiya akalla 200 na can tsare hannun ƴan bindiga ba a kai ga ceto su ba.

Wannan dalili ya sa dole gwamnatin Kaduna ƙarkashin Nasir El-Rufai ya ɗage komawa makarantu a jihar har sai an samu saukin hare-haren ƴan bindiga.

Share.

game da Author