APC da PDP, duk kanwar ja ce – In ji Attahiru Jega

0

A hira da Tsohon shugaban hukumar Zaɓe Attahiru Jega wanda a zamanin sa ne shugaba Buhari yayi nasarar kada Goodluck Jonathan a 2015 da BBC Hausa, ya yi korafin cewa cewa manyan jam’iyyun kasar nan biyu, APC da PDP duk baragurbin shugabanni ne ke dunkule a cikin su.

Akasarin waɗanda ke bisa kujerun mulki a kasar nan yanzu ba kasar bace a gabar su

” Yanzu ku duba ku gani, kafin zuwan APC Yanzu ku duba ku gani, kafin zuwan APC jam’iyyar ta yi ta kurin zata saka ƙafar wando ɗaya da ɓarayin gwamnati amma kuma waɗanda aka yi wa zargin harkalla a baya idan suka tsunduma APC shikenan sun tsira.

Jega ya ce yin haka na nuna cewa ashe dai dama duk kanwar ja ce.

Jega ya ce tun a 1979 ya zama malamin jami’a a fannin kimiyyar siyasa. Hakannya bashi damar sanin fuk wata mas’aloli, kutunguila, da sauran su. ” Hakan ya sa na na yi nesa da jam’iyyun biyu na yi rajista a PRP”.

Share.

game da Author