ANA WATA GA WATA: Yan bindiga sun sace daliban makarantan Islamiya a Katsina

0

Yan bindiga sun sace daliban makarantar Islamiya a kauyen Sakkai, dake karamar hukumar Faskari jihar Katsina, kamar yadda rundunar ‘yan sandan jihar ta sanar.

Wasu mazauna kauyen Sakkai da suka zanta da wakilin PREMIUM TIMES HAUSA sun bayyana cewa bayan daliban da suka sace sun arce da wani malami giuuda daya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina, Gambo Isa ya bayyana cewa an sace daliban makarantar ne a lokacin da suke dawowa gida daga makaranta.

” Mutanen gari duk sun ga yan bindigan a lokacin da suke arcewa da yaran makarantan su 9 wanda dukkan su ba su wuce yan shekara 12 zuwa 19 ba.

” Yaran na hanyar su ta komawa gida daga makaranta ne. Ba a makarantar aka sace su ba. Sun gamu da yan bindigan ne a hanya a daidai su kuma za su shiga wasu kauyuka da ke kusa da makarantar, sai suka ga garabasar yara na tafiya gida suka tattara su a bisa baburan su suka nausa da su cikin kungurmin daji.

Wani mazaunin kauyen ya ce mutane sun hango maharan a lokacin da suke ficewa daga garin Faskari.

Ana kyautata zaton yan bindigan da ke karkashin rundunar marigayi gogarman yan bindiga, Dogo Nabajallah ne suka yi garkuwa da daliban.

Share.

game da Author