Ana ci gaba da ragargazar ‘ƴan bindigan da suka addabi mutanen Kaduna – El-Rufai

0

Kwamishinan tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana cewa jami’an tsaro na ci gaba da yi wa ƴan bindiga da maɓoyan su a dazukan Kaduna luguden wuta babu ƙaƙƙauta a faɗin jihar.

Aruwan ya ce dakarun tsaro sun kashe ƴan bindiga huɗu a samame da suka kai musu a har inda suka boye.

” Dakaraun tsaro sun kashe mahara huɗu a batakashin da suka yi a karamar hukumar Zangon Kataf. Sannan kuma an kashe wasu ‘yan bidigan a kududdufin dake Maikwandaraso, da ke karamar hukumar Igabi, Jihar Kaduna duk a ci gaba luguden wuta da ake yi wa mahara.

Wadanda aka kashe sun hada da Alili Bandiro, Dayyabu Bala, Bala Nagwarjo and Sulele Bala.

Gwamna Nasir El-Rufai, ya jinjina wa ayyuan da sojojin ke yi a dazukan dake kewaye da jihar inda nan ne maɓoyan ‘yan bindigan da inda suke tsare mutane idan suka yi garkuwa da su.

Sannan kuma ya shaida cewa nan ba da dadewa ba gaskiya za ta fito kowa ya san abinda ake yi.

Idan ba a manta ba gwamnatin Kaduna ta dakatar da komawa makarantun jihar saboda har sai ta ci ƙarfin bindiga da suka a addabi mutane da makarantun jihar.

Kafin gwamnati ta janye hutun, ɗalibai za su koma karatu ne ranar 9 ga wannan wata da muke ciki, wanda yayi daidai da yau litinin.

Share.

game da Author