An tsinci gawar limami a cikin mota, kwana ɗaya bayan cigiyar sa

0

Al’ummar garin Atiba a yankin Ijebu cikin Jihar Ogun na cikin halin jimamin mutuwar limamin garin, Mushafau Bakare, wanda aka tsinci gawar sa a ranar Laraba, kwana ɗaya bayan bacewar sa.

Yayin da aka ga limamin bai dawo gida ba kamar lokacin da ya saba, an kira wayar sa, amma ta na kashe. Bayan an yi cigiya ba a kan shi ba, sai aka kai rahoto ofishin ‘yan sanda.

Iyalan mamacin sun ce kwata-kwata ba su kawo batun garkuwa da liman Mushafau ba.

Sai dai kuma ‘yan sanda sun tsinci gawar sa a cikin mota a hanyar Ƙaramar Hukumar Odegbolu.

Kakakin Yaɗa Labarai na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan sandan sintiri sun wuce motar sa a kan titi a tsaye, kuma ba su san motar ƙirar Highlander Jeep ta sa ba ce.

“Sai da su ka dawo, su ka motar tsaye a inda ta ke, sannan su ka fita su ka duba, su ka ga gawar sa a ciki.”

Ya ce an bincika babu alamun murɗe shi ko shaƙe shi, kuma babu wani rauni a jikin sa.

Sai dai kuma an fi alaƙanta mutuwar ta sa da ciwon hawan jinin da ke damun sa, wanda aka ce ta yiwu ciwon ne ya tashi a lokacin da babu mai kai masa ɗauki kusa.

An dai rufe shi bayan yi masa jana’iza, kuma ana jikan sakamakon da asibiti zai fitar daga baya.

Share.

game da Author