Shugaban Kwamitin Wutar Lantarki a Majalisar Tarayya, Magaji Aliyu, ya bayyana cewa mummunar manufar siyasa ce da wasu ɓangarorin gwamnati su ka cusa a harkar wutar lantarki ya sa Najeriya ta kasa samar da wadatacciyar wuta a ƙasar nan.
Aliyu ya yi wannan kakkausan jawabin a wurin taron shekara-shekara na ‘Yan Kwangilar Samar da Wuta a Karkara da aka yi ranar Laraba, a Abuja.
Aliyu ya ce haka kawai da rana tsaka ko a cikin duhun dare an ƙirƙiro wasu hukumomi a ƙarƙashin Ma’aikatar Samar da Wuta, ba tare da sanin Ministan Harkokin Lantarki ba.
Sama da sheksru 30 ɓangaren samar da wutar lantarki a ƙasar nan ya kasa cimma biyan buƙatar dalilin kafa shi. Kuma duk da rashin wadatacciyar wuta a ƙasar nan, kuɗin wutar sai daɗa ƙaruwa ya ke yi.
A shekarar da ta gabata, Ministan Makamashi Sale Mamman ya bayyana cewa Najeriya ta kafa manyan injina da za su iya samar da migawat 13,0000 na ƙarfin lantarki a ƙasar nan. Amma kuma har yanzu wadda ake samu ba ta wuce migawat 6,000 ba.
“Kamar yadda ku ka sani, mu na Majalisa ne domin mu yi doka, sannan mu riƙa sa-ido. Amma a gaskiya lamarin harkar wutar lantarki a ƙasar nan, ya na cikin babbar matsala saboda rashin ingantaccen tsarin tafiyar da ɓangaren.” Inji Aliyu.
Ya ce tilas a samu tsari sahihi wanda ‘yan siyasa za su ƙyale Ma’aikatar Samar da Wuta ta yi aikin ta na wadata ƙasar nan da wutar lantarki wadatacciya.
“Akwai fa wata sabuwar ma’aikata, wai ita Federal Power Company, wadda Ministan Samar da Wuta bai ma san da ita ba.
“Saboda haka ni ina ganin ‘yan siyasa na wuce gona iri a lamarin, kuma ‘yan Najeriya ne ke cutuwa.” Inji Honorabul Aliyu.
“Yanzu haka a sashen ‘Nigerian Bulk Electricity Trading Company’, ana ta kitimirmirar rikicin inda hukumar ya kamata ta kasance.Wasu na cewa a ƙarƙashin Ma’aikatar Samar da Wutar Lantarki. Wasu kuma na cewa a’a, a ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe ya kamata hukumar ta kasance.
“Haka ma Hukumar Hydropower Development Agency. Wasu na cewa a ƙarƙashin Fadar Shugaban Ƙasa, wasu kuma cewa ko dai a ƙarƙashin Ma’aikatar Samar da Wutar Lantarki?”
“Mun sha rubuta wa Shugaban Ƙasa wasiƙu, mu na jan, hankalin sa cewa kamata ya yi fa a riƙa yin komai a kan ƙa’ida. Amma mun wayi gari hukumomin samar da wuta, waɗanda ya kamata a ce su na ƙarƙashin Ma’aikatar Samar da Wuta, wasun su na ƙarƙashin Ma’aikatar Harkokin Kuɗaɗe, wasu kuma a ƙarƙashin Babban Bankin Najeriya (CBN). Ƙiri-ƙiri Ma’aikatar Samar da Wuta ba ta da hurumin kula ko sa-ido a kan su.
“Saboda haka kawai ni dai na yi imani cewa akwai wata maƙarƙashiyar da aka ƙulla a siyasance, domin a hana bunƙasa harkokin wutar lantarki a ƙasar nan.”
Aliyu ya ce bincike ya nuna ‘yan Najeriya da dama na biyan kuɗin wutar da ba su sha ko ba su yi amfani da ita ba.