An danƙara wa ‘yan sanda naira biliyan huɗu domin zuba fetur a motocin sintiri

0

Ma’aikatar Kula da Harkokin ‘Yan Sanda ta bayyana cewa an ware wa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Naira biliyan huɗu domin sayen man fetur ga motocin sintiri.

Ministan Harkokin ‘Yan Sanda Maigari Dingyaɗi ne ya bayyana haka a wurin wani taron da ya jiɓinci jami’an ‘yan sanda a Abuja.

Sanarwar da ya fito daga Kakakin Yaɗa Labarai na Ma’aikatar ‘Yan Sanda, ta ƙara da cewa dama akwai batun kashe kuɗaɗen a cikin kasafin 2021.

Dingyaɗi ya ce za a yi amfani da kuɗaɗen a dukkan sassan ‘yan sanda a faɗin jihohi 36 da Abuja, Babban Birnin Tarayya.

A cewar sa wannan ne karo na farko a aka taɓa bai wa ‘yan sanda muƙudan kuɗaɗen zuba wa motocin sintiri mai.

Daga nan ya ce Ma’aikatar Harkokin ‘Yan Sanda za ta ci gaba da dukkan ƙoƙarin ganin an inganta ayyukan aikin ‘yan sanda ta hanyar wadata su da kayan aiki da su ka haɗa da makamai, motocin sintiri, rigunan sulke, bindiga da albarusai da kuma ba su dukkan ƙaƙƙoƙin su.

Ya ce dama kuma Hukumar Gidauniyar ‘Yan Sanda (PTF) ta amince a sayo waɗannan kayan aiki. Dingyaɗi ya ce baya ga wannan, za a ƙara inganta ayyukan jami’an tsaron ta hanyar bada horo.

Share.

game da Author