Wata ɗalibar Sakandaren Chibok da ke hannun ‘yan Boko Haram tun cikin 2014, ta kuɓuta makonni kaɗan bayan da wata tare ɗan Boko Haram ɗin da ya riƙe ta a matsayin matar sa sun miƙa kan su ga sojoji.
Wadda ta kuɓutar a ranar Asabar mai suna Hassana Adamu, ta miƙa kan ta ga Sojojin Najeriya a garin Gwoza cikin Jihar Barno.
Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamnan Barno, ya bayyana cewa an gabatar da Hassana Adamu ga Gwamna Babagana Zulum a lokacin da ya kai ziyara a Gwoza, ranar Asabar.
Kakakin na Gwamna mai suna Isa Gusau ya fitar da sanarwa mai ɗauke da cewa, “Kwamandan Sojojin Birged ta 26 ne Burgediya Janar DR Ɗantani ya damƙa ɗalibar mai suna Hassana Adamu tare da ‘ya’yan ta biyu ga Gwamna Zulum.”
“An ɗamƙa su a hannun Zulum ne a lokacin da ya kai ziyara a Gwoza, inda daga can ya zarce Bama, ya na aiwatar da ayyukan jinƙai da bayar da tallafi.
“Dama kuma bai daɗe ba daga dawowa daga Arewacin Barno, inda ya shafe kwanaki biyar a can ya na raba kayan agaji da ayyukan jinƙai.”
Hassana ta na ɗaya daga cikin ɗaliban sakandaren Chibok su fiye da 200 waɗanda Boko Haram su ka gudu da su tun cikin 2014, a ranar 14 Ga Afrilu .
Ta kuɓuta daga ƙangin shekaru bakwai makonni biyu bayan da wata mai suna Ruth Pogu da aka kama su tare ta samu ‘yancin ta.
Pogu ta samu ‘yancin ta bayan lokacin da wani ɗan Boko Haram da ta ce shi ne ya aure ta bisa tilas ya miƙa kan sa a hannun Sojojin Najeriya a Bama, kilomita 49 daga Gwoza.